7 awanni baya
Shugaba Tinubu ya kuma umarci a dauki karin ’yan sanda da sauran jami’an tsaro da yawa. Sannan ya yi alkawarin nuna goyon baya ga jihohi da suka kafa rundunonin tsaron al’umma inda ya bukaci majalisar dokokin kasar ta gyara dokoki da za su bayar da damar kafa ’yan sandan jihohi.

