Harin makarantar St. Mary a jihar Neja: Iyaye na neman 'ya'yansu ido rufe
Har yanzu iyaye na ci gaba da neman ‘ya'yansu ido rufe bayan shafe kwanaki da sace ɗalibai da malaman makarantar St Mary’s Catholic da ‘yan bindiga suka yi a Jihar Neja. Kofofin makarantar sun kasance a rufe yayin da al’ummar yankin ke alhinin harin.