4 awanni baya
Babu dai wata alama da ke nuna cewa zai iya magance matsalar yunwa da talauci wadanda suka addabi al’ummar kasar.
Mai Magana da Yawun Shugaban Nijeriya Bayo Onanuga ya yi watsi da kalaman na dan takarar shugabanci kasa a zaben shekarar 2023, inda ya bayyana su da kalamai marasa kima. Mr Onanuga ya ce tsohon mataimakin shugaban kasar da mutanen da ke tare da shi idonsu ya rufe dangane da ci gaban da aka samu a kasar.