10 Satumba 2025
An soma gida madatsar ruwan ce a Kogin Nilu a 2011, sai dai wannan aiki ya jawo tayar da jijiyoyin wuta tsakanin Ethiopia da maƙotanta Masar da Sudan game da yiwuwar rage ƙarfin ruwa a Kogin Nilu.
Ana sa rai dam ɗin zai samar da fiye da wegawat 5,000 na lantarki, wato zai ninka yawan wutar lantarkin da Ethiopia take amfani da ita yanzu.