12 Satumba 2025
Masana suna cewa fara yaƙin neman zaɓe da wuri yana raba hankalin shugabannin da ke riƙe da muƙamai, kuma sakamakon hakan yana sanyawa ba sa iya mayar da hankali wajen yi wa al’umma aiki, sai su ɓige da tunanin yadda za su sake cin zaɓe. Shugaban Hukumar INEC Farfesa Mahmoud Yakubu ya koka kan yadda hukumar ba ta da hurumin hukunta wadanda aka samu da laifin fara yakin neman zabe da wuri.