22 Disamba 2025
Bayan wasu 'yan mintuna, jirgin sama-jannatin da ta shiga ya sauka cikin aminci a yankin hamada na Jihar Texas ta Amurka.
Benthaus ta zama gurguwa ne sakamakon tsautsayin da ta gamu da shi yayin hawa tsauni a shekarun baya. Tun daga lokacin, ta riƙa fafutukar kawar da shinge na tafiya sararin samaniya.

