22 Disamba 2025
Ƙasashe 24 ne za su fafata a gasar, kuma tuna mai masaukin bakin Maroko ta fara da ƙafar dama, inda ta lallasa Komoros da ci 2-0 a wasan farko na gasar da suka buga a rukunin A.
TRT Afrika Hausa za ta ringa kawo muku bayanai da labaran abubuwan da suke faruwa a gasar daga Maroko ɗin, wadda za a shafe kusan wata guda ana fafatawa.

