24 Disamba 2025
Mutum 2,000 aka rantsar a matsayin dakarun rundunar mai suna Neighbourhood Watch Corps, waɗanda za a rarraba su a faɗin ƙananan hukumomin jihar 44, kuma sun haɗa da mata 130 da maza 1,870.
Za a bai wa dakarun bindigogi don yaƙi da manyan laifuka da ake aiwatarwa a jihar.
Sannan gwamnan ya ƙaddamar da motocin hiluz 88 da babura 440 waɗanda aka bai wa rundunar tsaron jihar.

