10 Disamba 2024
Magoya bayan jam’iyyar hamayya ta National Democratic Congress (NDC) a ƙasar Ghana na ci gaba da murna sakamakon nasarar da ɗan takararsu na shugaban ƙasa kuma tsohon shugaban ƙasar Ghana, John Dramani Mahama ya samu a zaɓen da aka gudanar a ƙarshen mako.
Masu sharhi sun soma tsokaci kan dalilan da suka sanya jam’iyya mai mulki ta New Patriotic Party (NPP) ta sha kaye a zaɓen, kamar yadda za ku ji ƙarin bayani a wannan bidiyo.

