| Hausa
An ƙaddamar da dakarun tsaro na jihar Kano
01:29
An ƙaddamar da dakarun tsaro na jihar Kano
Gwamnan Jihar Kano Abba Kabir Yusuf ya ƙaddamar da rundunar tsaro ta jiha a ranar Talata, da nufin sa ido a kan tsaron unguwanni da yankunan jihar.
24 Disamba 2025

Mutum 2,000 aka rantsar a matsayin dakarun rundunar mai suna Neighbourhood Watch Corps, waɗanda za a rarraba su a faɗin ƙananan hukumomin jihar 44, kuma sun haɗa da mata 130 da maza 1,870.

Za a bai wa dakarun bindigogi don yaƙi da manyan laifuka da ake aiwatarwa a jihar.

Sannan gwamnan ya ƙaddamar da motocin hiluz 88 da babura 440 waɗanda aka bai wa rundunar tsaron jihar.

Ƙarin Bidiyoyi
Aljeriya ta yi dokar da ta ayyana mulkin mallakar da Faransa ta yi a matsayin laifi
Ziyarar ta'aziyyar ministan tsaron Turkiyya ga jami'an Libya
Ma'aikatan ceto na Turkiyya na bincike a wurin da jirgi ya fadi
Moses Simon da Akor Adams sun ce za su kara himma a wasan AFCON
Shirin wasan Super Eagles da Taifa Stars ta Tanzania
'Yahudawa 'yankama-wuri zauna sun mamaye harabar Masallacin Kudus
Matashin da ya bar shaye-shaye sannan ya dukufa wajen yaki da dabi'ar
Jama'a sun kwashi dankalin Turawa yayin zanga-zangar manoma
Gurguwa Injiniya ta kafa tarihin zuwa sararin samaniya
Shagalin bikin buɗe gasar AFCON 2025 a Maroko