A ranar Lahadi ne tawagar ƙwallon ƙafar Nijeriya, Super Eagles za ta kara da takwararta ta Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo a wasan neman shiga Gasar Cin Kofin Duniya ta 2020.
Kafin su kai ga wannan matsayin ƙasashen biyu sun samu nasara a wasannin da suke buga ranar Alhamis.
Nijeriya ta doke Gabon ne da 4-1, yayin da Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo ta doke Kamaru da 1-0.
Sai dai kuma tawaga ɗaya ce za ta wakilci nahiyar Afirka a ƙoƙarin neman cike gurbi ɗaya da ya saura da nahiyar za ta iya cikewa a Gasar Cin Kofin Duniya ta shekarar 2026.
Duk tawagar da ta yi nasara za ta wakilci Afirka a wasannin cike gurbin shiga Gasar Cin Kofin Duniya da za a yi a watan Maris na shekarar 2026.
Tarihin karawar ƙasashen biyu
Bari mu dubi tarahin karawar ƙasashen biyu a fagen tamaula da kuma tarihin ƙasashen biyu a Gasar Cin Kofin Duniya.
Ƙasashen biyu dai sau shida ne suka taɓa haduwa a tarihin ƙwallon ƙafa.
Nijeriya ta doke Kongo sau biyu inda Kongo ta doke Nijeriya sau uku, kuma ƙasashen suka tashi canjaras sau ɗaya.
Ranar 5 ga watan Nuwamban shekarar 1966 ne Nijeriya ta fara karawa da Kongo inda ta doke ta da 3-2.
Sai dai kuma Kongo ta ɗau fansa ranar 26 ga watan Nuwamban shekarar 1966 inda ta doke Nijeriya da ci ɗaya mai ban haushi.
Ƙasashen sun sake karawa ranar 27 ga watan Disamban shekarar 1966 inda Kongo ta sake doke Nijeriya da ci ɗaya da nema.
Tawagogin biyu ba su sake haɗuwa ba sai lokacin da suka kara ranar uku ga watan Maris na shekarar 2010 inda Nijeriya ta lallasa Kongo da ci 5-2.
Sai kuma shekarar 2015 inda Kongo ta doke Nijeriya da biyu da nema.
Karawar ƙarshe ita ce haɗuwarsu a ranar 28 ga watan Mayu inda suka tashi kunnen doki.
Muhimman ‘yan wasa
Duk da cewa ƙasashen biyu suna cike da ƙwararrun ‘yan wasan, akwai wasu ‘yan wasan da ake sa ran za su taka rawar gani a wasan da za a buga ranar Lahadi.
Victor Osimhen: Ɗan wasan gaban Galatasaray ta Turkiyya na kan ganiyarsa inda yake taimaka wa ƙasarsa Nijeriya da ƙungiyar da yake bugawa zura ƙwallaye a raga.
Ya zura ƙwallaye har biyar a raga a wasanni biyu na baya bayan nan da ya buga wa Nijeriya.
Aaron Wan-Bissaka da ke murza leda a ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta West Ham ya fara taka wa Kongo leda ne a watan Satumban shekarar 2025 inda ya ƙarfafa bayan tawagar ta Kongo.
Chancel Mbemba shi ne ya ci ƙwallo ɗaya tilon da ya bai wa Kongo damar nasara kan Kamaru fiye da minti 90 da fara wasa.
Mbemba dai yana taka leda a ƙungiyar Lille ta ƙasar Faransa kuma yana cikin waɗanda za a mayar da hankali a kansu a wasan da ƙasarsa za ta yi da Nijeriya a ranar Lahadi.
Benjamin Fredric ɗan wasa bayan ne da yake buga wasan aro a ƙungiyar Dender EH ta Belgium ɗan wasan ne mai shekara 20. Yana cikin ‘yan wasan da Nijeriya ke ji da shi da shi.
Ɗan wasan na baya bangaren dama ya taka rawa a nasarar da Nijeriya ta yi a kan Gabon inda ya hana ‘yan wasan Gabon irin su Aubermeyang sakat.
Arthur Masuaku da ke wasa a Sunderland na cikin ‘yan wasan da suka fi ƙwarewa a tawagar Kongo. Ɗan wasan na baya ya yi suna wajen iya kai hari daga baya.
Akor Adams: Ɗan wasan gaban Nijeriya ne da ke taka leda a ƙungiyar Sevilla ta Sifaniya. Shi ya fara zura ƙwallo a ragar Gabon a karawarta da Nijeriya. Yana cikin ‘yan wasan da manazarta za su fi mayar da hankali a kansu ranar Lahadi.
Axel Tuanzbe: Dan wasa ne da ke taka leda a ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Burnley da ke Ingila. Ya buga wasanni tara cikin 10 da tawagar ta Kongo ta buga a wasannin neman shiga Gasar Cin Kofin Duniya.
















