Zuwa Gasar Kofin Duniya ta 2026: Abin da ya jawo rashin nasarar Nijeriya a karawarta da DRC
WASANNI
4 minti karatu
Zuwa Gasar Kofin Duniya ta 2026: Abin da ya jawo rashin nasarar Nijeriya a karawarta da DRCJamhuriyar Dimokradiyyar Kongo ce ta jiƙa wa Nijeriya aiki a wasan neman tikitin zuwa Gasar Kofin Duniya a 2026.
Zuwa Gasar Kofin Duniya ta 2026: Abin da ya jawo rashin nasarar Nijeriya a karawarta da DRC
17 Nuwamba 2025

Ta tabbata dai Nijeriya ba za ta halarci babbar Gasar Ƙwallon Ƙafa da za a yi a kasashen Mexico da Amurka da kuma Kanada ba wacce za a yi a shekara mai zuwa.

Jamhuriyar Dimokradiyyar Kongo ce ta jiƙa wa Nijeriya aiki a wasan neman tikitin zuwa Gasar Kofin Duniya a 2026.

Tawagar Super Eagles ta Nijeriya ta yi rashin nasarar ne a hannun tawagar The Leopards ta Jamhuriyar Dimokradiyyar Kongo da ci 4-3 a bugun fanerati bayan an tashi wasa 1-1 a birnin Rabat na kasar Morocco.

Kasar Jamhuriyar Dimokradiyyar Kongo tana cike da farin cikin ci gaba da kaasancewa cikin kasashe kalilan da za su ci gaba da neman zuwa babbar gasar wacce rabon da kasar ta halarta tun shekarar 1974, wato lokacin da ake kiran kasar da Zaire.

Sai dai ita Nijeriya ta rasa damar zuwa wannan babbar gasa ne a karo na biyu a jere saboda rashin nasarar da ta yi ranar Lahadi.

Duk da cewa tawagar Super Eagles ta yi koci har guda uku tun daga fara wasannin neman zuwa Gasar Kofin Duniya zuwa yanzu wato tsawon shekaru biyu kenan da suka wuce, haƙar kasar ba ta cim ma ruwa ba.

Masana harkokin wasanni da dama suna ganin tawagar Super Eagles ba ta taka rawar gani ba a yawancin wasannin neman zuwa wannan babbar gasa da aka buga kuma sakamakon hakan ne ya sa kasar ta kasa kai labari.

Abin da ya faru a jiya Lahadi da tawagar Super Eagles kamar tarihi ne ya sake maimaita kansa saboda Gasar Kofin Duniya da aka yi a kasar Qatar a 2022 inda nan ma Nijeriya ba ta samu tikitin halarta ba.

An fadada yawan kasashen da za su halarci gasar daga 32 zuwa 48 kuma nahiyar Afirka za ta samu wakilcin kasashe tara maimakon gurabe biyar da ake warewa nahiyar a baya.

Wannan ya sa a farko aka rika kyautata zaton cewa duk rintsi Nijeriya za ta samu tikitin zuwa gasar.

Masani kan harkokin wasanni Malam Mansur Abubakar ya shaida wa TRT Afrika Hausa cewa idan Nijeriya tana so ta magance samun irin wannan matsala a nan gaba, to dole sai ta rika shiryawa gasar shekaru masu yawa kafin lokacin gasar.

Ya ce Nijeriya ba ta fara shirye-shiryen tunkarar gasar ba sai ana gab da farawa wanda hakan a cewarsa yake haddasa tarin matsaloli ciki har da kasancewar ’yan wasan ba su saba da salon wasan junansu ba.

Malam Mansur ya ce kasashen da suka ci gaba a kwallon kafa kamar Jamus da kasar Faransa, suna fara shirye-shiryen tunkarar gasar ne shekaru masu yawa kafin fara wasannin neman tikitin zuwa gasar.

Masanin ya ce Jamus, wacce ta halarci gasar a shekarar 2014 a Brazil kuma har ta lashe kofin gasar ta fara shiryawa samun wannnan nasara ne tun a shekarar 2002 lokacin da ta yi rashin nasara a hannun Brazil da ci 2-0 a wasan karshe.

Malam Mansur ya ce tun daga nan ne kasar ta zage damtse ta kafa wasu sabbin makarantun horas da yara kanana kwallon kafa a duk fadin kasar.

A cewarsa wannan dalilin ne ya sa kasar ta samu nasarar lashe kofin gasar a shekarar 2014 wato shekaru 12 bayan daukar wannan mataki.

Masanin wasannin ya ce idan Nijeriya tana son ta yi zarra a kwallon kafa, to akwai bukatar gwamnati ta dauki irin wannan mataki na yin renon yara kanana wadanda zuwa gaba za a ci amfaninsu ta fuskar kwarewarsu a tamaula, watakila ma kasar ta kai matakin da ba ta taba kai wa ba a gasar.

Sannan ya ce yana da muhimmancin gaske Hukumar da ke Kula da Harkokin Kwallon Kafa a Nijeriya (NFF) ta rika cire son zuciya wajen zakulo zaratan ’yan wasa wadanda za su rika wakiltar kasar, yana mai jaddada cewa ya kamata a rika mayar da hankali wajen zakulo kwararrun ’yan wasan kamar yadda kasashen da suka ci gaba a fannin kwallon kafa suke yi.

Ya ce tabbas akwai ’yan wasan da suke taka leda a tawagar Super Eagles kuma cancanta ce ta kai su ga hakan, kuma ya ce akwai wasu ’yan wasan da ke tawagar da ba su cancanci shiga tawagar ba.

 

Rumbun Labarai
Za a iya dakatar da Ronaldo buga wasanni biyu bayan ya samun jan kati
Kotu a Jamus ta goyi bayan danwasan da aka kora kan goyon bayan Falasdinu
Shugaban Barcelona ya gwale Messi kan yiwuwar komawarsa Barca
Hukumar ƙwallon ƙafar Sifaniya ta maye gurbin Lamine Yamal da Jorge de Frutos
Yves Bissouma: An kwashe wa danwasan Tottenham fam 800,000 daga asusun banki
Kocin Man United ya mayar wa Ronaldo martani kan sukar halin da kungiyar ke ciki
'Agent' ya saka wa dan wasan Tottenham bindiga a ka don ya tursasa shi
Tawagar Portugal za ta saka jesin karrama tsohon ɗan wasanta bakar fata
Mutum 41,000 daga kasashe 126 ne suka shiga wasan tseren sassarfa na Istanbul karo na 47
Yadda kwazon Yamal a filin wasa ya ragu saboda ciwon matsematsi
Da gaske ne Barcelona za ta nemi Victor Osimhen don maye gurbin Robert Lewandowski?
Kotu ta umarci Barcelona ta fito da takardun biyan dala miliyan 9 ga wani rafari
Yamal zai kashe $16m don sayen gidan da Pique da Shakira suka zauna
Mohamed Salah ya cire Liverpool daga shafukansa na sada zumunta bayan wasansu da Frankfurt
Osimhen, Salah, Hakimi: Jerin sunayen ‘yan wasan da ke takarar gwarzon shekara na CAF
‘Yan Nijeriya uku za su taka leda a Gasar Zakarun Turai ranar Laraba
Ronaldo ba zai je India buga wasan Al-Nassr da Goa ba
Alonso ya yaba wa Vinicius kan janyo wa 'yan wasan Getafe biyu samun jan kati
Messi ya jajanta wa tawagar Argentina bayan Morocco ta doke su, ta ɗaga Kofin FIFA U20
Morocco ta ɗauki kofin duniya na ‘yan ƙasa da shekara 20 bayan ta doke Argentina