AFCON: Jerin 'yan wasan Afirka da za su ƙaurace wa Gasar Firimiya
WASANNI
3 minti karatu
AFCON: Jerin 'yan wasan Afirka da za su ƙaurace wa Gasar Firimiya‘Yanwasa fiye da 40 ne za su iya kauracewa gasar Firimiya ta Ingila don wakiltar kasashensu na Afirka a gasar AFCON da za a yi a Morocco, daga 21 ga Disamba zuwa 18 ga Janairun 2026.
Za a fara AFCON 2025 daga 21 ga Disamba zuwa 18 ga Janairun 2026 / Reuters
8 awanni baya

Akalla kungiyoyi 16 daga cikin 20 na gasar Firimiya za su yi rashin zaratan ‘yan wasan da za su bakunci Marocco don kare mutuncin kasashensu a Gasar AFCON, wadda ita ce mafi alfarma a fagen kwallon kafa a nahiyar Afirka.

Zuwa yanzu dai ba duka kasashe ne suka fitar da jerin ‘yanwasan da za su wakilce su a AFCON ba, kafin a san ainihin yawan ‘yanwasan da su bar Firimiya. Amma ga jerin kungiyoyin, da kuma ‘yan wasa da za su iya rasawa.

Sunderland ita ce za ta fi kowa rasa zunzurutun ‘yan wasa har 7. Akwai Bertrand Traore da zai buga wa Burkina Faso.

Sai Arthur Masuaku da Noah Sadiki na Congo DRC. Sai Simon Adingra na Ivory Coast, Chemsdine Talbi na Morocco, Reinildo na Mozambique, da Habib Diarra na Senegal.

‘Yanwasa 5 ne za su bar Wolverhampton su je wakiltar kasashensu, Tolu Arokodare na Nijeriya, Emmanuel Agbadou na Ivory Coast, Jackson Tchatchoua na Kamaru, sai Marshall Munetsi da Tawanda Chirewa ‘yan Zimbabwe.

Crystal Palace za ta iya rasa Christantus Uche da zai jone da Super Eagles ta Nijeriya. Sai Ismaïla Sarr na Senegal, Cheick Doucouré na Mali, da Chadi Riad na Morocco.

Ita ma Nottingham Forest za ta iya rasa Ola Aina da Taiwo Awoniyi na Nijeriya, da Ibrahim Sangaré da Willy Boly na Ivory Coast.

Manchester United ta kwan da shirin rasa Bryan Mbeumo na Kamaru, Amad Diallo na Ivory Coast, da kuma Noussair Mazraoui na Morocco.

‘Yan wasan Nijeriya guda 3, Alex Iwobi, Calvin Bassey, da Samuel Chukwueze za su bar Fulham don zuwa Morocco.

Tawagar Congo DRC za ta dauke Axel Tuanzebe daga Burnley. Afirka ta Kudu za ta dauke Lyle Foster, yayin da Tunisia za ta dauke Hannibal Mejbri.

Tawagar Senegal za ta kwashe Iliman Ndiaye da Idrissa Gueye daga Everton. Sannan Morocco za ta kira Adam Aznou don buga gasar.

Omar Marmoush zai bar Manchester City don komawa Masar, sai Rayan Aït-Nouri ya jone da tawagar kasarsa Algeria.

Brentford za ta rasa Frank Onyeka dan Nijeriya, da kuma Dango Ouattara dan Burkina Faso. Yves Bissouma na Mali, da Pape Matar Sarr na Senegal za su bar Tottenham Hotspur.

West Ham United za ta rasa Aaron Wan-Bissaka na Congo DRC, da El Hadji Malick Diouf na Senegal.

Kungiyoyi masu rasa ‘yanwasa dai-dai su ne Liverpool da za ta rasa Mohamed Salah na Masar. Evann Guessand na Ivory Coast zai bar Aston Villa. Brighton & Hove Albion za ta rasa Carlos Baleba na Kamaru. Bournemouth ta rasa Amine Adli na Morocco.

Ke nan jimillar kungiyoyin gasar Firimiya su 16 ne za su rasa ‘yan wasan Afirka yayin gasar AFCON, inda kungiyoyi 4 kacal ne za su tsira, wato Arsenal, Chelsea, Leeds United, da kuma Newcastle United, wadda danwasanta guda, Yoane Wissa ya gaza samun gayyata daga kocin Congo DRC.

Rashin zaratan ‘yanwasan na tsawon wata guda zai tilasta wa kociyoyin kungiyoyin da abin ya shafa, su sake lale a tawagoginsu, don cike gibin da tafiyar ‘yan Afirkan zuwa gasar AFCON zai bari.