Damar da ta rage wa Nijeriya ta halartar Gasar Kofin Duniya
WASANNI
3 minti karatu
Damar da ta rage wa Nijeriya ta halartar Gasar Kofin DuniyaHukumar ƙwallon kafa ta Afirka, CAF ta sanar cewa za a buga wasannin cike-gurbin ne a cikin watan Nuwambar shekarar nan.
Bayan gasar Kofin Duniya ta Rasha a 1018, Nijeriya ba ta je gasar Kofin Duniya da aka yi a Qatara a 2022 ba. / Others
15 Oktoba 2025

Duk da ruwan kwallayen da Nijeriya ta yi wa makwabciyarta Jumhuriyar Benin a wasan neman tikitin zuwa Gasar Kofin Duniya a ranar Talatar nan, tawagar Super Eagles din ba ta samu cancantar zuwa gasar ba kai-tsaye, wato akwai sauran aiki a gaba.

A Rukunin C da Nijeriya ke ciki, Afirka ta Kudu ce ta samu tikitin zuwa gasar kai-tsaye bayan da ta doke Rwanda da ci 3-0.

Afirka ta Kudu ta hada jimillar maki 18 ne daga wasanni 10, yayin da Nijeriya da Benin kowanensu ke da maki 17.

Nijeriya ta samu damar zuwa matakin gaba na sake fafatawa don neman shiga gasar, saboda ta fi Benin yawan kwallaye, bayan da ta doke Benin din ci 4-0 a birnin Uyo na Jihar Akwa Ibom da ke kudancin kasar.

Tauraron dan wasan Super Eagles wanda ke buga wa Galatasaray ta Turkiyya, Victor Osimhen shi ne ya zura kwallaye uku na farko a ragar Benin.

Frank Onyeka, wanda ke buga wa Brentford ta Ingila, ya zura kwallo ta hudu ana gab da tashi wasan. Kuma ita ce ta bai wa Nijeriya damar zuwa matakin gaba a fafutukar neman buga gasar Kofin Duniya.

Sakamakon kwazon da wasu kasashe suka nuna amma ba su kai ga samun tikitin gasar kai-tsaye ba, shi ya sa za su je matakin buga wasan neman dama ta biyu (play-off).

Kasashen su ne: Nijeriya, Gabon, Kamaru da Jamhuriyar Dimokuradiyyar Kongo (DRC) su ne suka samu wannan dama daga nahiyar Afirka.

Hukumar ƙwallon kafa ta Afirka, CAF ta sanar cewa za a buga wasannin cike-gurbin ne a cikin watan Nuwambar shekarar nan.

Ta sanar cewa Morocco ce za ta karɓi bakuncin wasannin domin fitar da kasa daya da za a haɗa ta da wata kasar daga wata nahiyar, domin tantance gurbi ɗayan da ya rage na shiga gasar.

Nijeriya za ta kara ne da Gabon, yayin da Kamaru za ta kara da Jamhuriyar Dimokradiyyar Kongo.

Idan Nijeriya ta yi nasara za ta yi gaba ta hadu da Kamaru ko Jamhuriyar Dimokradiyyar Kongo.

Kuma daga nan ne za a samu kasa daya daga Afirka wadda za ta kara da wata kasa daga wata nahiyar. Kuma duk wadda ta yi nasara, to ta samu gurbin zuwa babbar gasa ta duniya.

Masana harkokin wasanni suna ganin akwai sauran jan-aiki sosai a gaban tawagar Super Eagles.

Kuma sai ta ci gaba da nuna jajircewa da hazaka kamar yadda ta nuna a wasansu da Benin, idan har da gaske tana son zuwa wannan babbar gasa da za a yi a kasashen Amurka da Canada da kuma Mexico.

An fadada yawan kasashen da za su halarci gasar daga 32 zuwa 48, kuma nahiyar Afirka za ta samu wakilcin kasashe tara da kuma damar karin guda, maimakon gurabe biyar da ake warewa nahiyar a baya.

Kuma wannan dalilin ne ya sa wasu masana da dama suke ganin cewa tawagar Super Eagles ba ta da wani uzuri, idan suka gaza zuwa wannan babbar gasa, saboda ganin yadda damar zuwa gasar ta karu sosai ga kasashen Afirka.

Watakila ma hakan ne ya sa har kasashe kamar Cape Verde wadda ba ta taba halartar gasar ba, ta samu tikitin zuwa gasar karon farko a tarihi.