NEMA ta nemi mazauna birnin da "su yi matukar taka tsantsan saboda mamakon ruwan sama da za a ci gaba da yi. Hoto: Others

Mazauna birnin Legas da ke kudu maso yammacin Nijeriya na fama da mamakon ruwan sama tun bayan da aka shafe awa 11 ana tafka ruwan a ranar Lahadi, lamarin da ya kawo ambaliya a gidaje da tituna da ma kasuwanni.

Hotuna da bidiyoyi da aka yada a shafukan sada zumunta sun nuna yadda ƴan kasuwa suke ta kokarin kwashe dukiyarsu da ambaliyar ke kokarin wucewa da su.

Sannan an ga wasu bidiyoyin na yadda fasinjoji suke rububin fita daga motoci ta taga sakamakon yadda ruwa ke kokarin shanye kan ababen hawan.

Hukumar ba da agajin gaggawa ta Nijeriya NEMA ta nemi mazauna birnin da "su yi matukar taka tsantsan saboda mamakon ruwan sama da za a ci gaba da yi.

‘’Ban taba ganin tashin hankali irin wannan ba," wata mazauniyar birnin ta shaida wa TRT Afrika.

‘’Ina zama ne a unguwar Ojo a Lagos kuma ruwan sai da ya kai har ƙuguna. Illahirin titin ruwa ne yake ambaliya. Dukkan shagunan da ke unguwar Ojo ambaliya ta shanye su," ta ce.

NEMA ta ce mafi yawan gidajen mutane a birnin Legas ba su cika ƙa'idar gine-gine masu inganci ba. Hoto: Others

Yankunan da abin ya fi shafa su ne Babban Titin Lagos-Badagry da Ebute-Ero da Lagos Island da Satellite Town da Trade Fair da Abule-Ado, da kuma Titin Ago Palace, duka a cikin birnin Legas.

NEMA ta ce mafi yawan gidajen mutane a birnin ba su cika ƙa'idar gine-gine masu inganci ba - wasu ma a kan hanyar ruwa aka gina su - lamarin da yake ta'azzara ambaliya tsawon shekaru.

Fuskantar hatsari

Hukumar ba da agajin gaggawa ta Nijeriya ta ce ita ma tana cikin shirin ko-ta-kwana kan yiwuwar samun ambaliyar ruwa a kasar, musamman a jihar Adamawa ta arewa maso gabashi, inda jami'ai ke tsoron cewa Kogin Binuwai zai tumbatsa.

Karfafa sa idon da ake yi a jihar na daga cikin "ƙoƙarin rage tasirin da ambaliyar za ta iya jawowa a yankunan da ke kusa da Kogin Binuwai ɗin."

Mutum uku ne suka mutu a ambaliyar da aka yi a baya-bayan nan, inda NEMA take ci gaba da gargadin yankunan da ke kan hanyar da ambaliyar ke afkuwa da cewa su kasance cikin shiri tare da barin wajen zuwa inda ake sa ran abin ba zai shafa ba.

TRT Afrika