Ana yawan jin karar harbi da hare-hare ta jiragen sama cikin dare tun da aka fara gwabza fada a Sudan sama da makonni biyar kenan ana haka Photo: AFP

Wasu shaidu a Khartoum, babban birnin Sudan sun ce an ci gaba da gwabza fada tare da kai hare-hare ta sama mintoci kadan bayan yarjejeniyar tsagaita wuta ta mako guda da ta fara aiki a ranar Litinin da daddare.

An yi ta ganin hayaki na tashi sakamakon harbe-harbe da kone-kone a birnin.

Janar-Janar biyu da ke yakar juna sun sanya hannu kan jerin yarjejeniyar tsagaita wuta a baya amma ba su yi tasiri ba.

Sai dai Amurka da Saudiyya da suka shiga tsakanin wurin kulla wannan yarjejeniyar sun bayyana cewa ta sha bamban da na baya saboda "bangarorin ne suka rattaba hannu" kuma sun ba da tabbacin bin tsarin "tsagaita wuta".

Wani ganau a kudancin Khartoum ya bayyana cewa an kai hari ta sama, sannan aka yi shiru, jim kadan kafin yarjejeniyar tsagaita wutar ta fara aiki.

Ana jin shiru da nutsuwa daga hare-hare da harbin bindiga cikin dare tun da aka fara yakin da aka kwashe sama da makonni biyar ana gwabzawa a Sudan.

A ranar Litinin ne mazauna birnin Khartoum, wadanda suka makale, suka cika da dokin samun damar zuwa ga 'yan uwansu da suka tsere don samun agajin jinkai.

Sai dai sun bayanna cewa babu wata alama da ta nuna cewa mayakan na shirin tsagaita wuta, inda suka ba da rahoton luguden wuta da aka yi ta yi ta jiragen sama a ranaku ta 37 a jere.

“Jiragen yaki sun yi ta kai hari kan unguwanninmu’’ a cewar wani mazaunin a Khartoum Mahmoud Salah el Din a hirarsa da da kamfanin dillancin labaran AFP.

A ranar 15 ga watan Afrilu ne aka fara gwabza fada tsakanin rundunar sojin Sudan karkashin jagorancin Abdel Fattah al Burhan da kuma dakarun RSF da mataimakinsa Mohamed Hamdan Dagalo ke jagoranta.

A cewar yarjejeniyar mai shafi bakwai da Amurka ta fitar, bangarorin da ke fada da juna za su yi amfani da kwanaki biyu don sanar da dakarunsu kafin yarjejeniyar ta fara aiki a ranar Litinin tare da ba su “umarnin su bi doka”.

Amma Volker Perthes, wakilin Majalisar Dinkin Duniya a Sudan, ya shaida wa kwamitin sulhu na Majalisar cewa, "har yau ana ci gaba da gwabza fada kuma har yanzu sojin na harbe-harbe duk kuwa da alkawarin da bangarorin biyu suka dauka na tsagaita wuta".

Yayin da dakarun gwamnati ke kula da sararin samaniya sojinsu kadan ke kasa a tsakiyar birnin Khartoum, inda dakarun RSF ke kan mamaye tituna.

"Ba mu ga wata alama da ke nuna cewa dakarun RSF na shirin janyewa daga tituna ba," a cewar Salah el Din.

Kimanin mutane 1,000 ne aka kashe a cikin makonni biyar da aka kwashe ana fama da tashe-tashen hankula da suka jefa kasar cikin mawuyacin hali.

Fiye da mutane miliyan daya ne aka raba da matsugunansu daga ciki sama da mutane 250,000 ne suka yi gudun hijira ta kan iyakokin Sudan lamarin da ke kara haifar da damuwa ga zaman lafiyar yankin.

“Muna jin yunwa dukkanmu”

Sa'o'i kadan kafin yarjejeniyar tsagaita wutar ta fara aiki, Dagalo ya fitar da sakon murya ta kafar sada zumunta inda ya yi jawabi kan ire-iren cin zarafi da sojojinsa ke yi, kamar yawan sace-sacen kayayyakin jama'a da kai hare-hare a kan majami'u inda ya dora alhakin laifin kan "masu yunkurin juyin mulki" a cikin dakarunsa.

Ya shaida wa mayakansa cewa “ko dai mu yi nasara ko kuma mu yi shahada, amma nasara tamu ce.”

A wani taron kwamitin sulhu, wakilin Sudan da ke biyayya ga Burhan ya zargi rundunar RSF da aikata irin wannan laifi.

Duk da jarjejeniyar tsagaita wuta da aka yi a baya, fararen-hula sun dage tare da fatan ganin an mutunta jarjejeniyar, don ba da dama a shigar a shigar da kayayyakin agaji da ake bukata a kasar.

"Dukkanmu muna fama da yunwa, yara, tsofi, kowa yana jin yakin nan a jinkinsa. Ba mu da sauran ruwan amfani ," in ji Souad al Fateh mazaunin Khartoum a hirarsa da AFP, yana mai rokon bangarorin biyu su "samar da mafiya".

Sama da rabin al'ummar kasar kusan mutane miliyan 25 na bukatar agajin jinkai a cewar Majalisar Dinkin Duniyar.

"Ta hanyar tsagaita bude wuta ne kadai za a iya dawo wa da ruwan famfo, sannan a karshe na samu damar ganin likita domin ya kamata ina zuwa asibiti akai aki saboda ciwon sukari da hawan jini da na ke fama," in ji Khaled Saleh.

A cewar wasu mutane kamar Thuraya Mohammed da ke kudancin Khartoum, zai zama wata dama ta tserewa saboda, "Khartoum ba wurin da ya dace a yi rayuwa a cikinta ba ne domin an lalata komai."

Likitoci sun sha nanata cewa tsarin kiwon lafiya da ya riga ya fada cikin mumunar yanayi kafin farawar yakin, na dab da rugujewa baki daya a Khartoum da sauran wurare musamman yankin yammacin Darfur.

Shakku

A rahoton da MDD ta fitar ta yi nuni kan cewa, an kashe daruruwan mutane fararen-hula a El Geneina babban birnin Darfur, kuma a jawabin da ya yi a taron kwamitin sulhu na majalisar Perthes ya yi gargadi kan yadda "kabilanci da ake samu a rikicin na iya kara hura wuta wanda yin hakan ba karamin hadari zai haifa ba ga yankin".

Wani kazamin fada da aka yi Nyala, babban birnin Darfur ta Kudu a makon da ya gabata ya yi sanadiyar kashe mutane 28, kamar yadda kungiyar likitocin kasar ta bayyana.

Othman al Zein, wani mai shago a kasuwar Nyala, wanda aka sha kai wa hari da sace-sace, ya shaida wa AFP cewa "idan aka tsaigata wuta" zai bar birnin.

"Ko da yake ina shakkar za a aiwatar da hakan a dukkan fadin Sudan," in ji shi.

A watan Oktoban shekarar 2021 ne Burhan da Dagalo suka hada kai wajen yin juyin mulki da ya kawo cikas ga mika mulki ga farar-hula bayan hambarar da tsohon shugaban kasar Omar al-Bashir a 2019.

Daga baya kuma sai ko wannensu suka fantsama yakar juna wajen gwagwarmayar neman iko, ciki har da hadewar rundunar RSF zama sojin mai zaman kanta.

Andrew Mitchell, karamin minista a ma'aikatar harkokin wajen Birtaniya, ya shaida wa AFP a Geneva cewa "yana da matukar muhimmanci a samu tsagaita bude wuta da zai yi tasiri da kuma dorewa tare da komawa kan turbar siyasa."

TRT World