Atiku Abubakar shi ne ɗan takarar shugaban Nijeriya a Jam'iyyar PDP a zaɓen shekarar 2023. / Hoto: Atiku Abubakar

Tsohon mataimakin shugaban Nijeriya Atiku Abubakar ya caccaki Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu kan kamun ludayinsa dangane da mulkin Nijeriya.

Atiku ya bayyana haka ne a wata sanarwa da ya fitar a shafinsa na X inda ya zargi shugaban da gazawa wurin jagorancin ƙasar.

“Tinubu ya tsaya wasa yayin da Nijeriya ke neman nutsewa cikin kogin rashin tsaro.

A yi tunanin cewa babban kwamandan askarawa na ziyara wadda ba ta aiki ba a yayin da masu garkuwa da mutane suka kashe mace mai shayarwa da wata kaka a Abuja kan gaza biyan kuɗin fansa har miliyan 90 da kuma wasu sarakai biyu a Ekiti, da wasu bala’o’i da ke faruwa a Nijeriya,” in ji Atiku.

“Idan takalman Emilokan sun yi masa girma, ya janye gefe. Nijeriya ba ta buƙatar shugaba ɗan yawon buɗe ido. Kasar na bukatar shugabanci na awa 24 don tunkarar matsalar tsaro da tabarbarewar tattalin arziki, “ kamar yadda Atiku ya ƙara da cewa.

Sai dai fadar shugaban Nijeriyar ba ta mayar da martani kan zargin da Atiku yake yi wa shugaba Tinubun ba.

TRT Afrika