‘Gurguwar da maza suka yi wa fyade suka yi mata ciki sau biyu a Nijeriya’

‘Gurguwar da maza suka yi wa fyade suka yi mata ciki sau biyu a Nijeriya’

‘’Maza sun yi mani fyade na yi ciki sau biyu saboda sun ga ni gurguwar ce’’
Wadda ta gamu da ibtila'in fyade/ AA

Grace (ba ainihin sunanta ba ke nan) na ‘’tsoron maza’’ kuma ta ‘’daina yarda da su’’ bayan da aka yi mata fyade, ta yi ciki sau biyu sannan aka yi watsi da ita.

Grace ta zama gurguwa ce tun tana karama saboda kafarta ta shanye baki daya, sakamakon tangarda da aka samu wajen yi mata allurar rigakafi. Sanadiyar haka, tun shekaru da dama kawo yanzu, mai fama da larurar nakasar tana amfani da keken guragu. Akwai dai mutane kimanin muliyan 30 da ke fama da nakasa a Nijeriya daga cikin al’umar kasar kimanin muliyan 200.

Kamar nakasassu da dama, Grace kan fuskanci kyama da tsangwama da cin zarafi da kuma wariya a cikin al’uma.

To amma wani al’amari da ya matukar girgiza ta shi ne wanda ya faru a wata ranar Lahadi a cikin 2014. Lokacin shekararta 21.

A ranar, ta tafi majami’a kamar yadda ta saba a jihar Bayelsa da ke kudancin Nijeriya, wato inda ta ke zaune. To amma dawowarta gida ke da wuya, ba ta san dawan garin ba, sai wani matashi makwabcinsu ya kira ta zuwa gidansa, wai ta zo ta ‘’taimaka masa da wani abu na gaggawa’’ ba tare da ya fayyace mata takamaimai mene ne ba. Daga nan sai mutumin mai shekaru 30 da ‘yan kai, ya yi mata fyade.

‘’Mun yi ta gwagwagwa da shi, ina kuma yi masa magiya, amma bai saurare ni ba’’ inji Grace. Yayin da ta ke tuna abin takaicin, ta ce ‘’wannan shi ne lokacin da namiji ya taba kwanciya da ni rayuwata kuma na rasa budurcina.’’ Grace ta yi ciki sanadin lamarin na fyade.

Bayan da mai fyaden ‘’ya yi amfani da karfi ya sadu da ni’’ sai ya nemi afuwa yana cewa wai ‘’in yafe masa, aikin shedan ne.’’

Mai larurar ta kara da cewa ‘’na ji tsoron fada wa wani’’ cewa an yi mata fyade saboda fargabar matsalar nuna kyama a cikin al’umma. To amma shiru da Grace ta yi ya zo karshe bayan watanni, lokacin da aka tabbatar tana da ciki a sakamakon gwaji da aka yi bayan da ta yi kukan rashin lafiya. ‘’Ban san ina da ciki ba sai bayan wata shida’’ a cewarta. Daga nan ta ba iyayenta labarin fyaden.

Grace ta ce mutumin da ya yi mata fyaden bai musanta ba lokacin da ta shaida masa cewa ta yi ciki, to amma sai ‘’ya yi batan dabo’’ daga unguwar.

Bayan shekara bakwai, a 2021, Grace ta sake fuskantar makamancin wannan yanayi na fyade lokacin da wani makwabcinsu na daban, shi ma ya yaudare ta zuwa gidansa a kekenta na guragu.

Ta haifi gawawwaki ne a duka cikin guda biyu da ta samu sanadin ayyukan fyaden bayan tangardar nakuda a asibiti. Grace ta ce ‘’ni kaina na kusa mutuwa’’ a lokacin nakuda. A ciki na farko, likitoci sun ce ‘’jaririn ya dade ma da mutuwa a cikina.’’

’Ba zan taba yafe wa mazan da suka yi mani ciki ta hanyar fyade ba’

Matar mai nakasa ta ce ta yi tunanin kai wa ‘yan sanda rahoton fyaden da aka yi mata amma sai iyayenta suka ce kar ta yi haka domin ‘’bai wajaba ba’’ kuma ba su da kwarin gwiwar cewa za a yi adalci. A maimakon haka sai suka mayar da hankali wajen kula da cikin da kuma lafiyarta.

Wadda aka yi wa fyaden ta yi watsi da bukatar afuwa daga mazan da suka yi mata fyaden domin a cewarta neman afuwar abu ne da ba za ta iya fahimta ba. Ta yi imanin da gangan suka aikata, don haka ta ce ‘’ba zan taba yafe masu ba.’’

Grace dai daya ce tak cikin dimbin mata da ‘yan mata masu larurar nakasa da ke fama da matsalar fyade da cin zarafi a Nijeriya - lamarin da ke haifar masu da munanan illoli.

A cewar Majalisar Dinkin Duniya hadarin fyade da mata da yara mata masu larurar nakasa ke fuskanta ‘’ya kai ninki uku’’ na wadanda ba su da nakasa ke fuskanta, kuma ‘’sun fi yiwuwar fuskantar cin zarafi na tsawon lokaci da kuma raunuka masu tsanani.’’

Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres/ AA

Hukumar Kare Hakkin bil-Adama ta Nijeriya ta ce an kai mata korafe-korafe kusan 140,000 na lamuran fyade da sauran nau’o’in muzgunawa masu nasaba da bambancin jinsi daga shekara ta 2020 zuwa ta 2021.

Duk da cewa da wahala a iya tantance hakikannin adadin mata da yara mata da ke fama da matsalar fyade a Nijeriya, masalar ta zama ‘’ruwan dare’’ a kasar, a cewar mai fafutikar kare hakkin bil-Adama, Misis Martha Olufunke Osadare. Misis Martha ita ce shugabar wata kungiya wadda ba ta gwamnati ba ce mai suna Disability Support and Rehabilitation Centre, wadda ke kokarin kare hakkin masu larurar nakasa da kuma kyautata rayuwarsu a Nijeriya.

Ta ce masu fyade na ‘’fakewa da raunin masu nakasa’’ wadanda ‘’da kyar su ke iya fitowa fili su yi magana.’’ A cewar Misis Martha, akwai matsalar nuna kyama da tsangwama, kuma masu fyaden kan yi masu barazanar cewa za su dandana kudarsu idan suka kuskura suka fada wa wani. Saboda haka, ‘’ba a samun cikakken rahoto’’ na lamuran fyade.

Ita kuwa Grace wadda ta sha da kyar bayan an yi mata fyade, ta ce duk da cewa ta san hatta matan da ba su da larurar nakasa kan fuskanci fyade, to amma ta yi imanin cewa wadanda suka yi mata fyade sun yi amfani da kanacewarta ‘’marar kariya sosai.’’ A cewarta: ‘’Da ni ba mai larurar nakasa ba ce, to ina jin da ba su same ni cikin sauki haka ba.’’

‘Kurma kuma bebiya ‘yar shekara hudu da aka yi wa fyade a Kaduna.’’

A Nijeriya, ba baligai mata kadai irin su Grace ke fuskantar fyade ba. Su ma kananan yara masu larurar nakasa ba su tsira daga masu aikata fyade ba. Wata ‘yar makaranta kurma kuma bebiya na jinyar mummunan rauni da ta samu sanadin fyade da ake zargin wani baligi ya yi mata. Lamarin da ya shafi Ladi (ba sunanta na ainihi ke nan ba) ya faru ne a jihar Kaduna da ke arewacin Nijeriya kuma ya girgiza wandanda suka samu labarin faruwarsa.

Iyayenta sun fara shiga damuwa ne bayan da suka lura da motar makarantar su yarinyar ta yi jinkirin dawo da ita gida. A cewar mahaifinta, lokacin da aka dawo da ita daga bisani, sai ‘’aka ga ba ta da alamar kuzari’’ kuma jim kadan sai suka ga jini na zuba ‘’daga al’aurarta.’’ Da aka tambaye ta, sai ta yi amfani da salon maganar kurame, ta yi bayanin abin da ya faru, lamarin da ya kai ga kama direban motar makarantar. ‘’Yarinyar ta yi ta zubar da jini tsawon kwana tara’’ inji mahaifinta.

An kai Ladi asibiti inda likitoci suka shaida wa iyayenta cewa lamarin fyaden ya shafi cikin cikinta.

Iyayenta na zargin an yi mata fyaden ne ba domin jin dadi na jima’i ba, sai dai wata kila saboda tsafi. Mahaifin yarinyar wanda ya dugunzuma, ya ce ‘’satinmu biyu ba mu iya barci, kuma da kyar mu ke iya cin abinci.’’ Ya kara da cewa ‘’muna bukatar a yi wa wannan yarinya da babu ruwanta adalci.’’ Ladi dai ita ce ‘ya daya tilo a wajen iyayenta. Mahaifin ya ce ‘’wannan yarinyar ta fi mana komai daraja. Yarinya ce ta musamman’’ kuma ‘’mai basira matuka’’ duk da larurar da ta ke fama da ita. Ladi ta nuna tana da hikima da kuma sha’awar zane-zane abin da ya bai wa iyayenta kwarin gwiwa kan baiwarta.

A halin yanzu dai ana tsare da direban motar makarantar yana fuskantar tuhume-tuhume masu nasaba da aikata fyade, amma ya musanta. Sai dai lauyar da ke kare ta, Bukola Ajao, ta ce za su ci gaba da fafutikar shari’ar domin ‘’an lalata yarinyar’’ tana mai cewa raunukan da ke farjin yarinyar, wata ‘’shaida ce ta zahiri.’’

‘’Al’adar yin gum kan batun fyade a Nijeriya’’

Hukuncin fyade a Nijeriya dai shi ne daurin rai-da-rai a karkashin dokokin tarayya, amma dai jihohi suna da nasu dokokin. Misali a jihar Kaduna, an tanadi hukuncin dandaka ga duk baligi da kotu ta samu da laifin fyade ga yaro ko yarinya da ba su fi shekara 14 da haihuwa ba. To sai dai kuma, kawo yanzu ko mutum guda ba a dandake ba a karkashin dokar wadda ta fara aiki a shekara ta 2020. Hakazalika, ba a samu wani ci gaba na a zo a gani ba tun bayan da shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari ya sanya hannu kan dokar kare hakkin nakasassu a 2019 – dokar da ta haramta nuna wa masu larurar nakasa wariya ko kyama ko kuma cin zarafi musamman a lamura na al’uma ko na hukuma – wadda kuma ta tanadi hukuncin dauri ko tara.

Hukumomi dai na cewa suna kokarin magance matsalar fyade a kasar da kuma kare hakkin mata da ‘yan mata masu larurar nakasa. Kwamishinar Ayyukan Kyautata Rayuwar bil-Adama da Lamuran Zamantakewa ta jihar Kaduna, Hajiya Hafsat Muhammad Baba, ta shaida cewa lallai ‘’har yanzu ana samun jinkiri a tsarin shari’a’’ amma dai gwamnati na iya kokarinta domin inganta lamarin.

Kwamishinar Harkokin Mata ta jihar Kaduna Hafsat Mohammed Baba/ Hoto daga shafinta na Facebook

Jami’ar gwamnatin ta ce wani kalubale kuma shi ne ‘’al’adar yin gum’’ game da matsalar fyade wato yadda wadanda aka ci zarafinsu ko kuma danginsu kan yi shiru kuma ba su kai rahoto ga hukuma. To amma Hajiya Hafsat ta ce sannu a hankali ana samun ci gaba wajen kawar da wannan al’ada saboda wayar da kan jama’a da ake yi. Ta ce: ‘’Muna farin ciki yanzu karin mutane na fitowa fili suna magana.’’

A cewarta, mata da yara mata masu nakasa na fuskantar cikas na musamman idan aka far masu. ‘’Ba su iya gudu’’ domin imma dai ‘’gurguwa ce ko makauniya.’’

Masu fafutikar kare hakkin bil-Adama na cewa wani kalubale da ke yin cikas ga samun nasarar hukunta masu fyade shi ne batun kawo shaida wanda ke da wahala da kuma bukatar taka-tsantsan. Mai kokarin kare hakkin nakasassu, Misis Martha Olufunke Osadare ta ce wajibi ne a kara himma wajen fadakar da al’umma kan hakkin masu larurar nakasa da kuma mutunta su.

Misis Martha ta kara da cewa kamata ya yi gwamnatoci su karfafa gwiwar masu larurar nakasa ta fuskar tattalin arziki da inganta tsarin ilminsu. A cewarta, wannan zai taimaka wa nakasassu su rika yanke managartan shawarwari kan rayuwarsu tare da martaba. Game da batun fyade ko cin zarafi, ta ce matakan za su taimaka masu su fahimci cewa ‘’suna da ikon hawa kujerar na-ki kan duk abin da ba su so.’’

TRT Afrika