Dakarun Nijar/ Hoto/AFP

Hukumar yaƙi da ta'addanci da sauran miyagun laifuka ta Jamhuriyar Nijar, SCLCT/CTO ta sanar da kama mutum kusan 773 da take zargi da hannu a ayyukan ta'addanci da tsageranci da kuma sauran laifuka.

Hukumar ta bayyana cewa ta samu wannan nasarar ce a cikin watanni ukun farkon wannan shekarar ta 2024.

Sanarwar hukumar ta ce jami'an tsaro na rundunonin sojojin Nijar daban-daban da suka haɗa da Opération Niyya da Opération Almahaou Opération Faraoutar Boushiya da Opération Shara da Opération Damisa daga jihohin Diffa da Tillaberi da Maradi da Agadez da Tahoua da Dosso ne suka yi nasarar kama mutanen.

Cikin zargin da ake yi wa mutanen har da na taimaka wa ƴan ta'adda da kayan abinci ko man fetur.

Sannan akwai kuma wadanda ake zargin su da garkuwa da mutane don neman kuɗin fansa da satar dabbobi da masu fataucin ƙwaya da makamai musamman akan iyakokin ƙasar.

Babbar cibiyar yaƙi da ta'addanci ta kasar ta bayyana cewa 78 daga cikin mutum 773 da ta kama ƴan asalin ƙasashen waje ne.

Kazalika hukumar ta ce daga cikin mutum 773 ɗin cikin watanni uku tuni ta miƙa takardun 372 gaban shari'a don su fuskanci hukunci.

TRT Afrika