Sanata Abdul Ningi

Majalisar dattijan Nijeriya a karkashin jagorancin shugabanta Godswill Akpabio ta dakatar da Sanata Abdul Ningi a ranar Talata, bisa zargin da ya yi na cewa an yi cushe na kasafin kudin 2024 na Naira tiriliyan 3.7.

An dakatar da Sanata Abdul Ningi mai wakiltar Bauchi ta Tsakiya har tsawon wata uku, bayan da aka yi wani zama da aka yamutsa hazo a zauren majalisar, kamar yadda kafar watsa labarai ta Channels ta rawaito.

Wani mamba a kwamitin kasafin kuɗi a majalisar dattawa, Jimoh Ibrahim ne ya fara gabatar da ƙudirin dakatar da Ningi na tsawon wata 12, bisa zarginsa da ba da bayanai ba daidai ba waɗanda suke daidai da aikata babban laifi, da kuma hargitsa zaman lafiya a Majalisar Dokoki da ma ƙasar baki ɗaya.

Wasu ‘yan majalisar kamar Sanata Asuquo Ekpenyong sun goyi bayan ƙudurin Ibrahim din.

Amma Ekpenyong, ɗan majalisa mai wakiltar Cross River ta Kudu da kuma Sanata Abdulfatai Buhari daga Oyo ta Arewa sun roƙi a rage tsawon dakatarwar zuwa wata shida da uku.

Akpabio, wanda ya bayyana laifukan Ningi a matsayin "manya", ya gudanar da wata ƙuri'a da baki inda mafi yawan 'yan majalisar suka amsa amincewa da dakatar da Ningi na tsawon wata uku.

TRT Afrika