Nijeriya da Afirka ta Kudu sun ne kasashen da suka fi karfin tattalin arziki a nahiyar Afirka. Hoto/NTA

Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu ya tattauna da Shugaban Afirka ta Kudu Cyril Ramaphosa a New York, inda yake bukatar kasashen biyu mafi girman tattalin arziki a Afirka su kara hada kai domin bunkasa tattalin arzikinsu.

Shugabannin na Afirka biyu sun hadu gabannin taron Babban Zauren Majalisar Dinkin Duniya wanda za a soma a wannan makon, a wata sanarwar hadin gwiwa da suka fitar.

“Za mu iya hada kanmu ta yadda duka za mu amfanar da jama’ar mu,” kamar yadda Tinubu ya bayyana, inda ya kara da cewa duka kasashen za su iya hada gwiwa ta fannin hakar ma’adinai da sadarwa domin “samar da ayyukan yi”.

Gwamnatin Shugaba Tinubu ta cire tallafin mai wanda ta ce kasar na matukar kashe kudi a kai da kuma cire takunkumin da gwamnatin baya ta saka kan hada-hadar kudaden waje.

Shugaban ya lashi takobin farfado da tattalin arzkin kasar wanda yake fama da bashi da hauhawar farashi.

Shugaba Ramaphosa a nasa bangaren ya jinjina wa tsare-tsaren farfado da tattalin arziki wanda Shugaba Tinubu yake kan yi, inda ya yi alkawarin cewa Afirka ta Kudu za ta hada kai da Nijeriya.

Neman habaka tattalin arziki

“Mu ne kasashe biyu mafi girman tattalin arziki a nahiyarmu kuma yana da kyau mu kara yaukaka dangantakar tattalin arzikinmu, musamman ta fannin yarjejeniyar kasuwanci maras shinge,” in ji Ramaphosa.

“Muna so mu ga Nijeriya da Afirka ta Kudu sun yi aiki kan abubuwa da dama saboda a duk lokacin da muka hada hannu, muna yin tasiri matuka a duniya ta hanyar matsayar da muke dauka ta hadin gwiwa,” a cewarsa.

Tinubu ya kuma bukaci Afirka ta Kudu da ta bi sahun Najeriya wajen yin kira ga yin garambawul ga cibiyoyin hada-hadar kudi na duniya domin taimaka wa Afirka wajen yakar talauci da tabarbarewar tattalin arziki.

TRT Afrika