An saka dokar hana fita a Kano jim kadan bayan alkalan kotun sun yanke hukunci. Hoto/Kwankwasiyya

Babban mai binciken kudi na Jam’iyyar NNPP ya caccaki alkalan da suka yi hukuncin shari’ar Kano bisa kalaman da suka yi game da jam’iyyar da ‘yan jam’iyyar.

A wata sanarwa da Ladipo Johnson ya fitar, ya nuna rashin jin dadinsa game da yadda alkalan suka yi amfani da ‘munanan kalamai’ a kansu a lokacin da suka yi hukuncin da ya bai wa Nasiru Yusuf Gawuna na Jam’iyyar APC nasara.

A hukuncin da alkalan suka yi a ranar Laraba, Mai Shari’a Benson Anya ce “Ina amfani da wannan damar domin yin tir da gungun masu jajayen huluna wadanda ke kama da ‘yan ta’adda, inda suka kore mu daga Kano tare da saka rayukanmu cikin fargaba.Mun yi amannar cewa Allah kadai ke ba da mulki.

Sai dai a martanin da Jam’iyyar NNPP ta mayar, ta ce wadannan kalaman ba su dace a ce sun fito daga alkali kuma mai kare doka ba.

Labari mai alaka: Masu jajayen huluna ne suka kore mu daga Kano: Alkalai

“Ba shakka, kalaman batanci da cin mutunci da tsinuwa da Mai Shari’a Benson Anya ya yi sun wuce ka’idojin Shari’a, hakan ya nuna alamun yana da ra’ayin wata jam’iyya sakamakon yadda yake nuna kyama ga shugabanni da mambobin NNPP.

Ya jaddada cewa Jam’iyyar NNPP za ta dauki matakan da suka dace wadanda suka hada da gabatar da korafi kan alkalan a hukumar kula da alkalai ta Nijeriya kan kalaman da alkalan suka yi da kuma daukaka kara kan hukuncin da alkalan suka yanke wanda ya cire Abba Kabir Yusuf daga gwamna.

Ya jaddada cewa suna da karfin gwiwa kan cewa za a yi musu adalci a Kotun Daukaka Kara don karfafa imanin mutane a bangaren shari’a da dimokuradiyya.

Kalaman da alkalan da suka yanke hukuncin shari’ar Kano suka yi tana da nasaba da barazanar da wasu daga cikin ‘yan Jam’iyyar NNPP suka yi wa alkalan, daga ciki har da Kwamishinan Kasa da Tsare-Tsare, Adamu Kibiya.

Sai dai jim kadan bayan wannan barazanar, gwamnan na Kano ya sallami kwamishinan da ya yi wannan barazanar.

TRT Afrika