Rikicin Boko Haram ya yi sanadin mutuwar fiye da mutum 40,000 sannan ya raba sama da mutum miliyan biyu da muhallansu / Hoto: AFP

Rikicin da aka gwabza tsakanin mayakan Boko Haram da na kungiyar da ke da alaka da Islamic State a Takfin Chadi ya yi sanadin mutuwar fiye da mutum 60, a cewar kungiyar da ke yaki da masu ikirarin jihadi da kuma mazauna yankin a ranar Litinin.

Fafatawa tsakanin bangarorin biyu ta kazance daga ranar Juma’a zuwa Asabar da suka gabata lokacin da mayakan ISWAP suka yi wa dandazon ‘yan Boko Haram kwanton-bauna a yankin Tafkin Chadi da ya hada kasashen Nijeriya da Nijar da Kamaru da kuma Chadi, kamar yadda wata majiya ta shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP.

Cikin wadanda suka mutu har da masunta da matan Fulani da mayakan Boko Haram suka sace, a cewar wasu majiyoyi.

Kungiyoyin biyu sun kwashe shekaru suna fafatawa don nuna karfin iko, inda suke yawan gumurzu tun bayan da ISWAP ta balle daga cikin Boko Haram a 2016 kuma ta karfafa ikonta a yankin.

Fada tsakaninsu ya yi kamari ne tun bayan mutuwar shugaban Boko Haram a 2021 yayin wata fafatawa a dajin Sambisa da ke karkashin ikonsa.

Mutumin da ya gaje shi ya ki mika wuya kuma ya tsere tare da mambobinsa zuwa tsibiran da ke Tafkin Chadi.

"An soma fafatawa ne da misalin karfe 4 na yamma kuma aka ci gaa da gwabza fada har ranar Asabar da safe inda kwale-kwale guda tara na kungiyar Boko Haram da dukkan mayakan da ke cikinsa suka nutse a ruwa," in ji Ibrahim Liman, wani shugaban kungiyar da ke yaki da kungiyar da ke ikirarin jihadi a yankin.

"Gaskiyar magana idan aka ce mutum 60 ne suka mutu an rage adadinsu.

Kwale-kwale tara sun nutse a ruwa, ka ga hakan ya nuna cewa mutanen da suka mutu za su zarta 60, babu ko shakka. Mun san yadda wadannan masu tayar da kayar baya suke cika kwale-kwale idan za su yi tafiya don kaddamar da hare-hare.

"Kuma idan aka yi la'akari cewa gomman mutanen da mayakan Boko Haram suka sace suna cikin kwale-kwalen, ka ga adadin yana da yawa," a cewar Liman.

Ya kara da cewa "mambobin ISWAP sun kama mayakan Boko Haram takwas ko da yake wasu daga cikin kwale-kwalen sun tsere" daga harin da aka kai musu a yankin Kaduna Ruwa.

Abubakar Alka, wani mazaunin yankin da aka sace masuntan da ke cikin kwale-kwalen, ya ce "kiyasi ne kawai" da aka ce mutum 60 ne ruwa ya ci su.

Kabiru Habu, shi ma wani shugaban kungiyar da ke yaki da masu tayar da kayar baya, ya ce: "Babu tabbacin adadin mutanen da suka mutu sakamakon fafatawar amma a bayyana yake cewa sun zarta 60.

"Ruwa ya ci dukkan mutanen da ke cikin kwale-kwale guda tara. Ko da a ce kowane kwale-kwale yana dauke da mutum 10, ka ga kusan mutum 100 sun mutu kenan. Kuma mun san cewa mayakan nan suna cusa mutane fiye da kima a kwale-kwale idan za su je kai hari."

AFP