Tunde Onakoya: 'Dan Nijeriya da ke daf da kafa tarihi a gasar Guiness World Records a fannin wasan Dara ‘Chess’/ Hoto: shafin X na Tunde Onakoya

Mataimakin shugaban Nijeriya Kashim Shettima da wasu gwamnonin jihohi da ofishoshin jakadanci wasu ƙasashe sun bi sahun milliyoyin mutane a ciki da wajen Nijeriya wajen jinjina da ƙarfafa gwiwa ga fitaccen ɗan wasan dara ''Chess'' Tunde Onakoya.

Matashin yana ƙoƙarin kafa tarihi a kundin nuna bajinta na Guinness World Record a fannin wasan dara mafi daɗewa - inda zai kwashe awa 58 ba tare da ya sha kaye ba - a dandalin Times da ke birnin New York na Amurka ya kuma samu goyon baya da jinjina daga ciki da wajen ƙasar.

A ranar Laraba ne Onakoya ya fitar da sanarwar fara gasar mafi daɗewa a shafinsa na X, inda ya yi wa wasan take da, "Game Time."

Ya ƙara da cewa, "Tun ma ba mu fara ba, tuni ƴan Nijeriya suka soma murnar nasarata."

Jinjina da ƙarfafa gwiwa

''Mista Onakoya ya kasance wata alama da ke nuna ƙwazo da tsayin daka na ƴan Nijeriya a gida da waje, kuma muna tare da shi yayin da yake jan hankalin duniya daga Dandalin Times Square na birnin New York a Amurka,'' a cewar mataimakin shugaban Nijeriya Kashim Shettima a saƙon ƙarfafa gwiwa da ya wallafa a shafinsa na X.

Sakon ya ƙara da cewa ''ka je ka kafa tarihi tare da rubuta sunanmu da zinare.''

Kazalika gwamnan jihar Legas Babajide Sanwo- Olu, ya bayyana goyon bayan al'ummar jiharsa ga ɗan wasan.

''Jihar Legas tana bayanka a daidai wannan lokaci da kake ƙoƙarin kafa tarihi a wasan dara mafi daɗewa a Dandalin Times Square da ke tsakiyar birnin New York,'' a cewar sakon da gwamnan ya wallafa a shafinsa na X

Ya ƙara da cewa ɗaukar labarin aikin da ka soma a Legas kan yara ƙanana zuwa wani mataki a duniya babbar shaida ce da ke nuna yadda bajinta da ƙwazo suke iya kai mutum ko ina.

Masanin tattalin arziki kuma fitaccen ɗan kasuwa Anthony Elumelu, ya ƙarfafa wa matashin gwiwa a sakonsa ta shafin X yana mai cewa '' Cigaba da zama abin alfahari musamman ga matasan Afirka! Muna goyon bayanka.''

Tunde Onakoya yayin da yake wasan dara da tsohon mataimakin shugaban Nijeriya Farfesa Yemi Osinbanjo/. Hoto:Shafin X na Farfesa Yemi Osinbanjo.

Tsohon mataimakin shugaban Nijeriya Farfesa Yemi Osinbajo ya jinjina wa matashin a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X inda ya ce, ''akwai yiwuwar a yi manyan abubuwa daga ƙaramin wuri." Ka bari ƙarfin kuzari na Dandalin Times Square ya ƙara fito da kwazonka, ɗan Nijeriya mai alfahari, ka nuna basirarka a dara. Mu duka muna bayanka - ka nuna wa duniya baiwar da Allah ya yi maka''.

A halin yanzu dai matashin yana ci gaba da fafatawa a gasar wadda aka fara da misalin karfe 10 na safiyar ranar Laraba, 17 ga Afrilu, kuma an shirya kammalawa da misalin karfe 8 na dare na ranar Juma'a 19 ga Afrilu.

Hallvard Haug Flatebo Sjur Ferkingstad na ƙasar Norway ne yake riƙe da kambin gasar a halin yanzu, inda a ranar 11 ga Nuwamba na shekarar 2018, ya lashe gasar bayan shafe a sa'o'i 56 da mintuna 9 da kuma sakan 37 a wasan.

Wane ne Tunde Onakoya?

Tunde Onakoya ɗan asalin Nijeriya ne wanda ya samu shaidar karatun Difloma a fannin Kimiyyar Na'ura mai ƙwaƙwalwa a Kwalejin Fasaha ta Yaba da ke jihar Legas inda ya samu lambar yabo bayan wakiltar makarantarsa a wasannin fasaha a Nijeriya sannan kuma a gasar Dara ta RCCG.

Kazalika ya lashe lambobin yabo da dama, waɗanda suka haɗa da ''Business Insider Award for Social Entrepreneur" na shekarar 2022 da "JCI Ten Outstanding Young Persons of Nigeria Award" wajen tallafa wa yara, da kuma lambar yabo ta "World Peace and Human Rights" ta shekarar 2022 da dai sauransu.

Ƙungiyar ''Chess in Slums Africa''

Onakoya yana da wata ƙungiya mai zaman kanta, Chess in Slums Africa, wadda ke amfani da wasan dara a matsayin hanyar tallafa wa yara marasa galihu don cim ma burinsu ta hanyar ba da ilimi kyauta da kayan makaranta da horo a fannin jagoranci.

Shirin ƙungiyar dai ya ja hankulan ƙasashen duniya sosai, sakamakon irin nasarorin da aka samu, inda aka tallafawa ƙananan yara sama da 10,000 marasa galihu a Legas tare da bai wa yara sama da 500 cikakken tallafin samun ilimi a makaratun cikin gida da na ƙasashen waje.

Ƙungiyar tana ƙoƙarin samar da makoma mai kyau ga kowane ɗan Afirka

TRT Afrika