Wata al'umma ta kafa wata kungiya domin farfado da karatun littattafai. Hoto/Getty Images

A cikin wata fitowa ta wani fim din Hollywood na soyayya da barkwanci, mai suna You’ve Got Mail, wanda dan wasa Meg Ryan ke ciki, mai sayar da littattafai Kathleen Kelly ta yi inkarin cewa “Idan kana karanta littafi a lokacin da kake yaro, zai zama wani bangare naka a rayuwa.”

Karatu na komawa wata al’ada idan aka saba da bude shafukan littafi wadanda ke dauke da kalamai masu ilmantarwa da nishadantarwa.

Da zarar mutum ya mayar da karatu wata dabi’a, zai rika fadada karatu a-kai-a-kai.

Kelly ta kasance mai yawan karatu wadda littafin Miklos Laszlos na 1937 mai suna Parfumerie ya bai wa kwarin gwiwa, ta ce ba ta ji dadi ba da ta ga bincike daban-daban na nuna cewa al’adar karatu na raguwa matuka a duniya.

Binciken ya kawo wasu dalilai da ake zargin su suka haddasa hakan wadanda suka hada da zuwan intanet da rashin mayar da hankali da rashin kyawun tattalin arziki da talauci da cin hanci da sauransu.

Rubutu a bango

Nijeriya - kasa mafi girman tattalin arziki a Afirka - na daga cikin kasashen da aka lissafa a jerin kasashen da ba su da dabi’ar karatu, kamar yadda wani rahoto na duniya ya bayyana.

Alkaluma daga Hukumar Karatu da Rubutu da Yaki da Jahilci ta Duniya sun nuna cewa kashi 38 na ‘yan Nijeriya ba su iya karatu da rubutu ba.

Hudu daga cikin yara goma da ke makarantun firamare a kasar ba su iya karatun littafi kamar yadda rahoton ya bayyana.

Wannan lamarin na ci gaba da ta’azzara duk da kokarin da gwamnati ke yi domin dakile hakan amma bai yiwu ba saboda cin hanci.

Sai dai wasu daga cikin al’ummomi da jama’a sun dauki aniyar magance wannan lamarin ta hanyar daukar wasu matakai.

Al’ummar Jenta da ke Jos babban birnin Jihar Filato sun kasance misali.

Sakamakon damuwar da suke da ita ta karancin masu ilimi, sai matasan al’ummar suka kafa wata kungiyar mai suna Jenta Read Initiative wadda ke bayar da ilimi da kayan karatu kyauta da zummar cusa akidar karatu a tsakanin jama’a musamman yara.

Christopher Manga wanda shi ne shugaban shirin, ya shaida wa TRT Afrika cewa shirin ilmantarwar bai zo da wuri ba.

An soma wallafa daya daga cikin littattafan Nijeriya mafi shahara a 1958. Hoto/Others

Lallashi sosai

“A takaice mun fito da wannan tsarin ne bayan mun yi la’akari da yadda mutanenmu musamman matasanmu suke abubuwan da suka saba wa zamantakewa. Mun gano cewa akasarinsu ko dai sun fice daga makaranta ne ko kuma wadanda ma ba su taba zuwa makaranta ba,” in ji shi.

“Mun yanke shawarar neman hanyar da za mu ba su ilimi kyauta domin kada mu ba su damar samun wata dama ta korafi. Babban kalubale ne daga farko ganin cewa ‘yan kadan daga cikinsu ne suka amince da wannan bukatar. Sai dai bayan an dade ana lallashi, sai muka shawo kansu domin su shiga cikinmu,” in ji Manga.

Manga da sauran abokansa masu fafutukar ilmantarwa na tattara mutane wadanda suka fahimci amfanin ilimi a ciki da wajen al’umma domin bayar da kyautar littattafai ga dakunan karatu.

Babban burinsu shi ne matasa da yara. “A gaskiya tafiyarmu ta yi nisa. A lokacin da muka fara, mun kai lokacin da mambobinmu suke amfani da dakunansu a matsayin dakunan karatu sakamakon ba mu da isassun wurare. A halin yanzu muna da gini kuma mun sayi fili domin fadadawa,” in ji shi.

Baya ga taimakon mambobi domin su ci gaba da karatu, dakunan karatun na bayar da rahoto na kwamfuta da kuma gabatrwa ta bidiyo ga yara a ranakun karshen mako.

Kamar yadda Manga ya bayyana, kungiyar Jenta Read Initiative ta gyara rayukan matasa da dama wadanda da sai dai su kasance marasa ilimi. Kamar yadda ya bayyana, “suna amfana da kansu da kuma al’umma baki daya”.

Tsarin na kara bazuwa

Haka lamarin yake a unguwannin Tudun Wada da Anguwan Rukuba da ke Jos. Matashin marubuci Wungakah Tongjal na jagorantar wani mataki na habaka karatu.

Littafinsa mai suna The University Libarary ya bayyana amfani da dama da dakunan karatu ke da su ga jama’a.

Haka kuma Tongal ya yi maganar mayar da dakunan karatu su zama masu jan hankali ta yadda za su sa mutane su farfado da dabi’ar karatu.

“Lamarin shi ne dakunan karatu ba an yi su bane kawai domin littattafai. Akwai wasu karin abubuwa fiye da ajiye littattafai,” kamar yadda ya shaida wa TRT Afrika.

Alkaluma sun nuna cewa kaso 40 cikin 100 na daliban firamare ba su iya karatu da rubutu a Nijeriya. Hoto/AP

“Wani ɓangare na manufar rubuta littafin sh ine magana kan hanyoyin da za a sa ɗakin karatu ya zama abin sha'awa da abin godiya. Dakunan karatu na jama'a a ƙasashe irin namu ba sa bayar da sha’awa, kuma akwai ƙarancin kulawa. Kayata wadannan wurare zai jawo hankalin mutane kuma ya sa su ƙara sha'awar karatu da ba da labari.”

Karin walwala

Tongjal ya samar da wata hanya ta musamman ta ilimi mai suna "Bookmathics" don karfafa wa matasa gwiwa domin karatun littattafai.

A cewarsa, aikin yana bayar da wani tsari na daban fiye da yadda koyarwa ta gada. "Ainihin manufar Bookmathics ita ce samun ilimin kimiyya da kuma godiya ga ilmantarwa, duka biyun za su sa matasa su zama masu koyo na rayuwa.

Ina so su ga ilmantarwa ba kawai wani abu ne na azuzuwa ba ko kuma irin wannan tsari na yau da kullum, amma tsari ne. wanda zai iya faruwa ta hanyoyi da siffofi daban-daban," in ji shi.

“Babbar manufar Bookmathics ita ce samun nasara wurin samar da ilimin kimiyya wadda za ta sa yara su zama masu karatu har abada. Ina so su dauki karatu ba wai abin da ke cikin aji kadai ba, amma wani abu da za a iya yi ta bangarori da dama,” kamar yadda ya bayyana.

Yana ganin koyarwa a waje na bayar da yanayi daban-daban ga dalibai tare ƙarfafa ƙwarewar koyo daban-daban.

Janet Farding, karkashin shirin Jarding Reading Garden and Resource Centre ta bayar da wurinta a kyauta ga mutanen da ke bukatar wuri mai natsuwa domin yin duk wani abu na ilimi.

Kara cusa son karatu a zukata

Kamar yadda ta bayyana, neman wurin wanda yake shiru na jawo hankalin wadanda suke bukatar kebantancen wuri domin aiki ba tare da kawar da hankali ba.

Jarding ta bayyana cewa matakin da ta dauka na tallafa wa wannan tsarin ya samo asali ne daga bukatarta ta karfafa gwiwar mutane su kara matsa kaimi domin karatu, wadda wata al’ada ce da take ganin ta ragu idan aka kwatanta da abin da ake da shi da baya.

“Karatun littafi abu ne wanda ya wuce a lokacin da muke tasowa. Yazu akwai abubuwan da ke dauke hankali da dama wadanda ke sa yara ba su son karatu. Don haka domin kara cusa son karatu a zukatan yara, mun kirkiro wani shiri mai ban sha'awa don hanzarta farfado da dabi'ar karatu a tsakaninsu su."

Bayan sarari da ke kwantar da hankali kamar yadda yake haɓaka jin daɗin karatu, cibiyar Jarding tana ba da shirin musayar littattafai don faɗaɗa shirin.

TRT Afrika