‘Yan majalisar dokoki na jam’iyyar PDP mai mulki a Jihar Ribas 27 sun sauya sheka zuwa jam’iyyar APC. Hoto: Daily Trust

‘Yan majalisar dokoki na jam’iyyar PDP mai mulki a Jihar Ribas 27 sun sauya sheka zuwa jam’iyyar APC.

Wani dan majalisar Enemi George ya shaida wa gidan talabijin na Channels cewa sun ɗauki matakin nasu ne ƙarƙashin jagorancin Martin Amaewhule a ranar Litinin yayin zaman majalisar.

Matakin nasu yana zuwa ne bayan shafe makonnin ana tataburza kan shugabancin majalisar tsakanin magoya bayan gwamna mai ci, Siminalayi Fubara da tsohon gwamnan jihar Nyesom Wike.

A watan Okotoba ne ɗan majalisa Amaewhule ya aika wa gwamnan jihar saƙon neman tsige shi tare da cire Ehie a matsayin shugaban masu rinjaye na majalisar. Sai dai kuma ba tare da ɓata lokaci ba wasu ƴan majalisar da ke goyon bayan Gwamna Fubara suka tsige Amaewhule daga matsayin shugaban majalisar inda suka naɗa Ehie.

Rikicin majalisar mai mamba 32 ya samo asali ne sakamakon rikicin da ke tsakanin Gwamna Fubara da tsohon gwamnan jihar, Wike, wanda a yanzu shi ne ministan babban birnin tarayyar Nijeriya, Abuja.

Wani bidiyo da Channels TV ya wallafa a shafinsa na X ya nuna yadda ƴan majalisar da suka sauya shekar a cikin mota suna riƙe da tutocin jam’iyyar APC suna kaɗa su, tare da rera waƙoƙin goyon bayan APC.

TRT Afrika