Ana bin kowane Ba'amurke $97,000 yayin da bashin da ake bin kasar ya zarta $33tr

Ana bin kowane Ba'amurke $97,000 yayin da bashin da ake bin kasar ya zarta $33tr

Bashin ya karu da dala tiriliyan daya a watanni uku tun watan Yuni.
An kara adadin bashin da AMurka take iya ci bayan ya kai dala tiriliyan $31. Hoto: AP

Bashin da ake bin Amurka a karon farko ya haura dala tiriliyan $33, wanda hakan ke nufin ana bin kowanne dan kasar dala 97,000.

Alkaluman Ma'aikatar Baitulmalin Amurka sun bayyana cewa bashin ya kai wani mataki mafi yawa a tarihin kasar, a yayin da ake tattauna wa kan kasafin kudi a Majalisar Dokokin Amurka.

Yawan bashin ya kai dala tiriliyan 32 a watan Yuni, inda a watanni ukun da suka gabata ya karu da dala tiriliyan daya.

Idan wannan yanayi ya ci gaba, bashin zai kai dala tiriliyan 34 nan da karshen shekarar nan.

Iyakance bashi

Amurka ta kai makurar bashin da take iya ci na dala tiriliyan 31.4 a ranar 19 ga Janairun 2023, inda Ma'aikatar Baitulmalin Amurka ta dauki matakan kar ta kwana don kauce wa wuce wannan adadi.

Bayan tattaunawa game da iyakar bashin da za a iya ci, an cimma matsaya a Majalisar Dokoki, kuma Shugaba Joe Biden ya sanya hannu kan dokar kasafin kudi a watan Yuni don kara yawan bashin da za a iya ci, don hana kasar fada wa halin kaka nika yi.

Ana hasashen akwai Amurkawa kimanin miliyan 340.

Bashin da ake bin kasar ya tattara dukkan basukan da Gwamnatin Tarayya ta ciwo a tarihin kasar.

AA