Kashu na cikin abubuwan da suka fi samar wa Nijeriya kudin shiga bayan danyen mai/Hoto:Reuters

Fannin noman kashu zai iya samar wa kasar Ghana dala miliyan 600 a shekara idan aka samar da yanayi mai nagarta ga masu noman kashu din a kasar, a cewar wani mai rajin habaka noman kashu a kasar, Raphael Ahenu.

Kamfanin dillancin labaran Ghana ya ambato Mista Ahenu na cewa kasar ta samu dala miliyan 340.7 ne kawai daga harkar kashu a shekarar 2020.

An ambato shi yana cewa “danyen ‘ya’yan kashu tan 110,000 zuwa tan 130,000 da kasar take samarwa a halin yanzu ba abin alfahari ba ne.”

Ya yi wannan kalaman ne a lokacin da ake kaddamar da shirin muryar manoman kashu a garin Sampa da ke lardin Bono a Ghana.

Ya yi kira ga gwamnatin kasar da ta mayar da hankali wajen cira da fannin noman kashu din gaba.

Masharhanta na ganin kasar Ghana za ta iya samun karin kudin shiga idan ta habaka noman bishiyar kashu/Hoto:Reuters

Mista Ahenu ya ce akwai bukatar gwamnatin kasar da ke yammacin Afirka ta habaka noman kashu a kasar don ta ci moriyar yadda ake neman ‘ya’yan kashu din a kasuwar duniya.

A cikin ‘yan kwanakin nan dai kasar tattalin arzikin Ghana ta shiga wani hali wanda ya sa ta karbi rancen dala biliyan uku daga asusun ba da lamuni na IMF daidai lokacin da take neman sake fasalin yadda za ta biya basussukan da ake bin ta.

Masana na ganin kasar na bukatar kara yawan kudin shiga domin ta karfafa tattalin arzikinta.

TRT Afrika da abokan hulda