Tsarin Consumer Credit wani tsari ne da ya zama jigo na bunƙasar tattalin arzikin duniya a wannan zamani. Hoto: State House

Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu ya amince a fara aiwatar da matakin farko na bai wa ƴan ƙasan basussukan abubuwan buƙata masu muhimmanci ƙarƙashin tsarin Consumer Credit Scheme.

Consumer Credit wani tsari ne da ya zama jigo na bunƙasar tattalin arzikin duniya a wannan zamani, wanda yake bai wa ƴan ƙasa damar bunƙasa yanayin rayuwarsu ta hanyar mallakar abubuwan buƙata masu muhimmanci, kuma su dinga biya a hankali tsawon lokaci.

Yana bayar da damar sayen muhimman abubuwa kamar su gidaje da ababen hawa da ilimi da tsarin lafiya don su ya ba su damar samun tsarin rayuwa mai inganci.

“Ta hanyar tsari mai kyau na biyan bashin, za a dinga tattara bayanai na bashin da mutane ke ɗauka, waɗanda za su sake buɗe musu ƙarin damarmakin samun ingantacciyar rayuwa.

"Bugu-da-ƙari, ƙaruwar buƙatun kayayyaki da ayyuka tana ƙarfafa masana'antun cikin gida da kuma samar da ayyukan yi,” a cewar sanarwar.

Mai taimaka wa Shugaba Tinubu kan harkokin watsa labarai Ajuri Ngelale a cikin sanarwar ya ce “Shugaban ya yi imanin cewa ya kamata kowane ɗan Nijeriya mai aiki tuƙuru ya samu damar tafiyar da harkokin zamantakewarsa cikin sauƙi, ta yadda wannan lamunin zai taimaka wajen cim ma wannan manufa.”

TRT Afrika