Wani rukunin masu zuba jari daga Koriya ta Kudu sun kammala shirin gina matatun mai hudu masu ikon tashe ganga 100,000 kowacce rana a yankuna daban-daban na Nijeriya, in Gwamnatin Tarayyar kasar.
Karamin Ministan Albarkatun Mai Heineken Lokpobiri, ya bayyana hakan a wajen taron Kungiyar Mamallakan Matatun Mai na Nijeriya da aka gudanar Legas.
Ya ce gwamnatin tarayya na karfafa gwiwar masu zuba jari kan su kafa matatun mai ta hanyar samar da budadden yanayi ga kowa.
Lokpobiri ya lura da cewa kwanan nan aka bayar da shaidar amincewa ga wasu kamfanoni, wadanda bai bayyana sunayensu ba.
"Muna karfafa gwiwar masu zuba jari su gina matatun mai ta hanyar samar da budadden yanayi. Kwanan nan aka bayar da amincewa don gayyatar wasu kamfanoni zuwa Nijeriya daga Koriya ta Kudu, wanda suke son samar da matatun man fetur masu ikon tace ganga 100,000 kowacce rana a yankuna daban-daban na Nijeriya."
Hadin kai tsakanin gwamnati da masu zuba jari
Karamin Ministan Albarkatun Man na Nijeriya ya kuma ce gwamnati da 'yan kasuwa masu zaman kansu na hada kai a bangarorin haka da sarrafa mai da iskar gas.
"...Wannan hadin kai zai bayar da damar a samar da kanana da manyan matatun man fetur a cikin Nijeriya," in ji Ministan.
Lokpobiri ya ci gaba da cewa wannan mataki zai haifar da mai ido, saboda Gwamnatin Tarayya ta shirya karbar masu zuba jari don samar da kananan matatun mai, wanda zai inganta samar da makamashi a kasar.
Ya ce "Hukumar Kula Haka da Sarrafa Mai da Iskar Gas ta samar da ka'idodji da sharuddan hakow ada jigilar mai domin samar da yanayi na gaskiya da tabbatar da matatun man cikin gida sun samu isasshen man."
An dauki matakan karfafa gwiwar masu zuba jari
Minista Lokpobiri ya kara da cewa baya ga hadin kai da masu zuba jarin, an dauki matakan karfafa gwiwa da garabasa ga masu zuba jari a fannin man fetur.
"Mun bayar da fifiko wajen aiki da masu ruwa da tsaki don tabbatar da aiwatar da shawarwarin Kwamitin Samar da Kananan Matatun Mai da manufar bayar da garabasa d akarfafa gwiwar mamallakan matatun mai na cikin gida, ta hanyar ta tabbatar da sun samu isasshen mai a matatunsu," ya fada wa mahalarta taron.
Ya kuma ce za su tabbatar da janye duk hannayen gwamnati a fannin man fetur dari bisa dari, tare da kuma tabbatar da an dauki matakan da za su saukaka wahalhalun da hakan zai janyo kan talakawa 'yan kasa.
Ya ce "Ma'aikatar ta samar da yanayin saukaka haraji da janye wasu ka'idoji wajen shigo da kayayyakin gina matatar mai, wanda wani bangare ne na shirinmu na mayar da Nijeriya mai dogaro da kanta kan sha'anin mai da kuma ta kasance cibiyar tace albarktun mai a Afirka."
A karshe Ministan ya jadda aniyarsu na ci gaba da yaki da matatun mai da ba sa bisa ka'ida, da kuma satar danyen mai da ake yi a Nijeriya.