Jami'an tsaro a kasashen Afirka da dama na yaki da ta'addanci. Photo others

Daga Firmain Eric Mbadinga

Majalisar dokokin kasar Mozambik, kasar da ta jajirce wajen kai hare-haren ta'addanci a cikin 'yan shekarun da suka gabata, ta amince da wani ƙudirin doka a baya-bayan nan na ƙara wajabcin aikin soja daga shekaru biyu zuwa biyar.

Gwamnatin Mozambique ta kafa hujja da wannan doka ta hanyar da ta dace na inganta tasirin sojojin da ke yaƙi da ta'addanci.

A cikin 2021, Burkina Faso ta kafa tsarin "Mai Yiwa Kasa Hidima don Ci Gaba" wanda ke buƙatar ma'aikatan gwamnati masu shekaru tsakanin 18 zuwa 30 su sami horon soja na wajibi na watanni uku.

Kasar Maroko ta bullo da irin wannan hidimar ne ta hanyar wata doka da aka kafa a shekarar 2019, yayin da a Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo, inda ake yawan samun hare-haren ta'addanci, hukumomin kasar sun yi la'akari da zabin aikin soja na dole a watan Disamban 2022 don samar da katangar yaƙi da ta'addanci.

Ana kallon zaɓen aikin soja a matsayin wata hanya ta inganta aikin dakaru a adadi da kuma inganci ta ɓangarori daban-daban a Afirka, inda 'yan ta'adda ke kashe dubaan rayuka a kowace shekara.

Daga Nijeriya zuwa Kamaru da Burkina Faso da Nijar da Mali, da ƙyar a samu wata ƙasa da ta tsira daga bala'in ta'addanci.

Asarar rayuka

"Ya zama wajibi fiye da kowane lokaci mu yi iyakacin kokarinmu, mu yi amfani da dukkan hanyoyin da za a iya magance ta'addanci," in ji Thibault Mayombo Nzengué, wani jami'in gudanarwa a Gabon, inda sabuwar gwamnatin ta mayar da shuga aikin soji wajibi.

Nzengué ya yi imanin cewa aikin soja na dole yana da amfani wajen tabbatar da tsaro ga kowa.

"Rundunar sojojinmu, musamman sojojin Afirka, suna fuskantar kalubale na albarkatun bil'adama. Samun 'yan gudun hijira ko 'yan kasa na gari da za su iya ba da amsa a yayin da aka yi kira, ko kuma a duk lokacin da aka yi taron jama'a, zai zama babbar kadara," kamar yadda ya shaida wa TRT Afrika.

Dr Arnaud Houénou daga kasar Benin, wanda ke da digirin-digirgir a fannin kimiyyar siyasa, kuma kwararre kan harkokin tsaro na Afirka, ya ce gabatar da aikin soja na tilas - kan kowace irin hujja - dole ne a gudanar da shi bisa tsarin doka.

"Batun shiga aikin soja na tilas bisa zargin yaƙi da ta'addanci ko kuma kare martabar yanki ya kamata ya zama matakin dimokuradiyya da ke mutunta 'yancin kai," in ji shi.

Dokta Houénou ya ba da shawarar cewa dole ne aikin soja ya zama wajibi na shari'a, wanda ke nufin cewa kafin a amince da shi, aikin dole ne ya kasance batu ne na dokar da majalisar ta kare kuma ta zartar, wanda kuma ya shafi kowa.

Za'a iya bayyana ma'anar ma'aunin shekaru bisa ga alƙaluman ƙasar. "Idan wata kasa ba ta mutunta wannan tsari ba, jama'a na iya yin shakku kan halaccin aikin soja na tilas," in ji Dokta Houénou.

Dangane da tsawon lokacin da wannan matakin na tilas ya dauka, wajibi ne Majalisar ta sanya iyaka, ta la'akari da barazanar.

Georges Ngoma, wani masani kan zamantakewar jama'a na Kongo da ke Kanada ya ce ''Ra'ayin zato ya kan yi hasarar sa a lokacin da gaskiyar ta'addanci ta kasance manufa.

Togaciyar da ta zama wajibi

Yayin da ake ganin an amince da ƙa’idar aikin soja na tilas, kamar yadda aka amince da shi, Ngoma ya nuna cewa akwai bukatar a yi wasu ’yan bangar wajen aiwatar da shi.

"Wasu nau'ikan mutane, kamar wadanda ke aiki a wasu sana'o'i da marasa lafiya ko nakasassu, ana ba su uzuri (ba a keɓe su) daga aikin soja na dole ba, amma, al'adar shiga aikin soja, wato kiran matasa da su yi aikin soja da tsaron kasa, yayi nisa daga zama al'adar yarda da juna," in ji masanin ilimin zamantakewa.

Asarar sojojin da aka yi a lokacin arangamar da sojoji ke yi da maƙiya na ciki da na waje na sa wannan al'ada na fuskantar babbar suka.

Souleymane Ouedraogo, wanda ke kula da harkokin hadin gwiwa a cikin hadakar kungiyoyin farar hula a Burkina Faso, ya ce ya zama wajibi hukumomi a kasarsa da ma fiye da haka, ka da su yi amfani da wannan matakin wajen rufe bakin masu ruwa da tsaki a al'umma ko 'yan adawa.

Har ila yau, da alama akwai yarjejeniya kan fa'ida da amfaninsa, inda wasu masu ruwa da tsaki suka dage cewa ya rage kawai zaɓi ɗaya ne a cikin da yawa.

Gwajin inganci

Dokta Houénou ya yi imanin cewa dole aikin soja na iya yin tasiri mai inganci da dabaru wajen tinkarar wannan barazana. "Samun ingantacecn tsarin ajiyar makamai yana da amfani ko yaushe," in ji shi.

An wajabta aikin soja a ƙasashe da yawa a cikin shekarun 1900 saboda yaƙe-yaƙe ko rikice-rikicen yanki, ko da yake yana da tasiri mai yawa.

Matakin ya kasance yana aiki a Amurka, alal misali, lokacin yaƙin cacar baka, lokacin da aka horar da maza masu shekaru tsakanin 18 zuwa 25 don kara girman matsayin soja idan an buƙata. Haka kuma aka yi a lokacin yakin duniya biyu.

Aljeriya wacce ta sami 'yancin kai daga Faransa bayan yakin 1954-1962, ta gabatar da aikin soja na tilas a shekarar 1968.

A cikin 2023, tare da ƙarin wurare masu zaman lafiya, ƙasashe da yawa sun yi watsi da aikin soja na dole.

TRT Afrika