Wani hoton jirgi mara matuki da ya nuna yadda iftila'in ambaliyar ruwan sama ya lakube gidaje da dama bayan fashewar wata madatsar ruwa a kauyen Kamuchiri da ke yankin Mai Mahiu a kasar Kenya. Hoto: Reuters  

Daga Sylvia Chebet

An ji ƙarar fashewar wata madatsar ruwa (Dam) a tsakar daren ranar Lahadi a ƙauyen Kamuchiri da ke yankin Mai Mahiu wanɗa ya kwararo ya zama tamkar kogi kuma ya lakume gidajen da dama.

Iftila'in ya shafi gidan Mercy Wairimu, inda ya shafe danginta yayin da suke barci.

"Ba na ganin sun samu damar farkawa saboda gudun ruwan," kamar yadda George Mwaniki, daya daga cikin ƴan'uwan matar da iftila'in ya shafa ya shaida wa TRT Afrika.

Ƙarfin gudun ruwan da ya taho da tarin wasu tarkace waɗanda suka haɗa da duwatsu da bishiyoyi ya baje kowane gida da ya tarar a kan hanyarsa.

“Ba zan iya hasashen irin wannan mumunan yanayin da suka shiga ba; gani nake yi kamar wani mafarki nake yi, ina ta tunain ta yadda ya faru?” a cewar Mwaniki.

Cikin duhu makwabta suka shiga cikin ruwan domin ceto iyalan Wairimu da wadanda abin ya shafa daga wasu gidaje waɗanda su ma suka rushe.

Warimu wacce ke da shekaru 30 a duniya tana da ‘ya’ya hudu, kuma ya zuwa wayewar gari, ana da tabbacin cewa ƴa'yanta da ɗan'uwanta da ita kanta duk sun mutu.

An yi nasarar ceto mahaifiyar Warimu wacce shekaru suka ja mata daga iftila'in kana tana samun kulawa daga raunuka da tashin hankalin da ta shiga.

“Rahotanni daga kafafen watsa labarai na ƙasar sun rawaito cewa kusan mutane 40 ne suka mutu amma tuni al’ummomin yankin suka samo gawwakin mutane 70, don haka munin lamarin ya wuce yadda aka sanar,” a cewar masanin kimiyyar sauyin yanayi Mwaniki wanda ya fito daga yankin da iftila'in ya faru.

''Akwai yiwuwar hana aukuwar wannan hatsarin,'' in ji Mwaniki, yana mai cewa: "an yi gargadi kan faruwar lamarin amma ba a dauƙi mataki akai ba."

Mazauna yankin sun hallara a wurin da ake gudanar da bincike da kuma aikin ceto bayan iftila'in ambaliyar a kauyen Kamuchiri da ke yankin Mai Mahiu na gundumar Nakuru. Hoto / AFP

Madatsar ruwan, in ji shi, ta lalace kimanin makonni biyu da suka wuce, amma hanyar jirgin kasa da ke wajen ta hana ruwan kwararowa sosai.

"Don haka, da a ce akwai waɗanda suka mai da hankali kan wannan lamarin, da ana da masaniyar cewa za a iya fuskantar wata mummunar barazana ta fashewar dam din kana a dauki mataki, amma sai aka gaza yin hakan,'' in ji shi.

"Lokacin da dam din ya fashe sai ya hadu da ruwan da ke kwararowa ta hanyar jirgin ƙasan, daga nan sai ruwan ya bi ta karkashi kana ya ratsa har zuwa yankin Mai Mahiu ya kuma haifar da barna sosai," a cewar Mwaniki.

Sai dai gwamnatin gundumar Nakuru ta ce, wata hanya ce da ruwa ke wucewa zuwa wani kogi na kauyen da ke kusa da dam dim ne ta toshe kana ta yi sanadiyar fashewar madatsar ruwan.

Duk da haka dai masanin kimiyyar sauyin yanayin, bai wani gamsu da hujjar ba bisa ga irin horo kan nazarin haɗura da kuma shirin takaita aukuwar iftila'i' da ke da shi.

“Babu wasu haɗura da suka faru. kawai dai tarin wasu ƙananan kurakurai ne da suka yi yawa,” in ji shi.

“Zan kira haka da kalubalen tsari domin ko da mun yi watsi da ilimin kimiyya wajen dauƙar shawarwari, akwai buƙatar daukar matakin farko a lokacin da dam din ya fara nuna alamun fashewa, ya kamata a ce mutane ko shugabanni su duba su kuma rage ruwan cikin dam din.”

Ma'aikatar yanayi ta Kenya ta yi gargadin kan cewa za a ci gaba da samun ruwan sama sosai har zuwa tsakiyar watan Mayu. Hoto / Reuters

Mummunan iftila'in da ya auku a yankin Mai Mahiu ya sake tuni da tashin hankalin da aka fuskanta bayan fashewar wani dam shekaru shida da suka wuce a gundumar na Nakuru.

Ruwa mai karfin gaske da ya taso daga madatsar ruwan Solai ya mamaye wani kauye gaba ɗaya, inda ya yi sanadin mutuwar mutane kusan 50 a cikin dare.

Mwaniki ya matukar nuna damuwarsa game da yadda har yanzu hukumomi da ƴan kasar ba sa ba da fifiko kan gargadin alamun sauyin yanayi da ake fitarwa.

Ana ci gaba da fuskantar barazanar muhalli a duniya, a kewayen yankin Mai Mahiu ana yawan sare itatuwa da bishishoyi da kan haifar da zantarewar ƙasa kusa da koguna sakamakon ruwan sama mai karfin gaske da ake fuskanta.

“Batun sauyin yanayi ne kawai. Yawanci muna samun kusan milimita 300 (na ruwan sama) a lokutan damina tsakanin watan Afrilu zuwa Mayu. Ya zuwa yanzu, ina tsammanin mun samu fiye da milimita 450. Don haka karin da aka samu ya kai kashi 50 cikin 100.''

A ƴan watannin da suka wuce ne, Kenya da sauran ƙasashen yankin kusurwar Afirka suka fita daga cikin wani mummunan yanayin fari da aka shafe shekaru uku ana fuskanta.

"Sauran rahotannin da nake tattarawa ko kuma nake ba da shawara a kai su ne na shekara mai zuwa, akwai yiwuwar mu iya komawa cikin yanayin fari," in ji Mwaniki.

Yana mai jaddada buƙatar a shawo kan mummunan barazanar sauyin yanayi na fari da ambaliyar ruwa da ke lalata muhalli da ci gaban rayuwa.

Yayin da yake karbar baƙuncin taron shugabannin kasashen Afirka a wannan mako a Nairobi inda mutane 10,000 da ambaliyar ruwa ta raba da muhallansu, shugaban kasar Kenya William Ruto ya bayyana cewa, matsalolin yanayi na bukatar haɗin kai don daukar matakan gaggawa.

“A yayin da muka taru a nan, a yanzu haka Kenya da yankin Gabashin Afirka na fuskantar mummunar yanayi na iftila'in ambaliyar ruwa da ya shafi al'ummomi da dama kana ya lalata ababen more rayuwa tare da janyo cikas ga tattalin arzikinmu gabaki ɗaya,'' a cewar shugaba Ruto.

Yana mai ƙarawa da cewa, ''A halin da ake ciki, yankin kudancin Afirka na fuskantar matsanancin fari da ya addabi kasashe kamar Malawi da Zambia da Zimbabwe.''

''A bara, an samu yanayin ya sauya, lamarin da ya nuna irin rauninmu a sauyin yanayi mai tsanani, "in ji shugaban.

A cewar masana kimiyya dai, wannan shi ne mafarin raɗadin iftila'in da ake fuskanta idan har ba a dauki mataki magance sauyin yanayi ba.

"A shekaru biyu masu zuwa, ba zan yi mamaki ba idan aka samu ranar da muka samu ruwan sama da ya kai milimita 600 zuwa 800 a lokacin damunar watannin Afrilu zuwa Mayu.

Don haka idan ba mu soma ɗaukar matakai ba tun daga yanzu kan yadda za a magance waɗannan ƙalubale, to tabbas akwai yiwuwar lamarin ya yi munin da zai fi haka,'' in ji Mwaniki.

TRT Afrika