Rahoton ya ce rashin aikin yi zai ci gaba da zama babban kalubale a kasar saboda tafiyar hawainiyar da tattalin arziki yake yi / Hoto: AFP

Masana tattalin arziki sun fara tsokaci kan sabon rahoton kamfanin kwararru na duniya KPMG, da ya ce rashin aikin yi a Nijeriya ya karu da kashi 41 cikin 100 a wannan shekarar ta 2023.

A cikin rahoton nasa na baya-bayan nan mai taken KPMG Global Economy Outlook report, H1 2023,’ KPMG ya ce rashin aikin yi zai ci gaba da zama babban kalubale ga kasar saboda tafiyar hawainiyar da tattalin arziki yake yi da kuma kasa samar wa mutane aiki yadda ya kamata a duk shekara.

Farfesa Abdullahi Sule-Kano, masani ne kan siyasar tattalin arziki a Jami’ar Bayero ta Kano, ya ce rahoton na KPMG na nufin har yanzu ba a samu mafita kan tabarbarewar tattalin arzikin Nijeriya ba.

“Duk da cewa gwamnati na fitar da rahotanni da bayanai cewa tana kokari na samar da ayyukan yi da shawo kan tattalin arziki, na fi ganin bayanan a matsayin farfaganda,” in ji masanin.

KPMG ya ce ana sa ran rashin aikin yi zai ci gaba da zama babban kalubale a shekarar 2023 saboda dalilai hudu kamar haka:

  • Rashin zuba jari sosai daga kamfanoni masu zaman kansu
  • Rashin masana’antu
  • Tafiyar hawainiyar da tattalin arziki ke yi
  • Da kuma gazawar tattalin arzikin wajen samar da aiki ga mutum miliyan hudu zuwa biyar da ke neman aiki a kowace shekara.

Kamfanin ya ce duk da cewa Hukumar Kididdiga ta Kasar NBS ta ce an samu kari na rashin aikin yi daga kashi 23.1 zuwa 33.3 cikin 100 a shekarar 2020, “mun yi kiyasin cewa wannan adadin ya karu zuwa kashi 37.7 a 2022 kuma zai ci gaba da karuwa zuwa kashi 40.6 a 2023.”

Dakta Isa Abdullahi, malami a sashen Tsimi da Tanadi na Jami’ar Kashere a Jihar Gombe da ke Nijeriya yana ganin ta’azzarar rashin aikin yi na da alaka da kalubalen da aka samu wurin hada-hadar kudi a bayan-bayan nan sakamakon sauya fasalin naira.

“Wannan lamarin ya jawo durkushewar sana’o’i manya da kanana,” in ji shi.

Matasa su ne suka fi yawa a Nijeriya, kasa mai yawan al’umma fiye da miliyan 200.

A duk shekara ana yaye miliyoyin dalibai daga jami’o’i da kwalejoji daban-daban a fadin kasar, wadanda bayan kammala hidimar kasa suke raja’a tare da mayar da hankali wajen neman aiki, musamman ma na gwamnati.

Kuma a mafi yawan lokuta irin wadannan matasa ba su faye tunanin neman wata hanyar ta dogaro da kai ta daban ba sai fatan samun aikin gwamnati, ko na gwamnatin ma “sun fi son mai maiko.”

Me ke jawo karuwar rashin aikin yi a kasa?

Kamar yadda alkaluma suka nuna, Nijeriya kasa ce mai dumbin arziki na albarkatun kasa, musamman man fetur wanda da shi kasar ta fi dogara.

To amma duk da hakan, rashin ayyukan yi a tsakanin al’ummar kasar na ci mata tuwo a kwarya.

Ga wasu manyan dalilai da masana ke ganin suna jawo karuwar rashin aikin yi:

A mafi yawan lokuta mutane ba sa faye mayar da hankali kan dogaro da sana'o'in hannu ba don inganta rayuwarsu / Hoto: TRT Afrika

  • Rarraunan tattalin arziki
  • Rashin ingantaccen tsarin ilimi da habaka dabaru
  • Mummunan yanayi a fannin aiki
  • Cin hanci
  • Rashin bin tsari wajen daukar ma’aikata.

Ta yaya za a magance yawaitar rashin aikin yi a tsakanin al'umma?

Wannan ce gaba mafi muhimmanci da ya kamata gwamnatoci da su kansu al’ummar kasa su mayar da hankali wajen nazarin su, in ji masana irin su Dakta Isa.

“Dole shugabanni da al’ummar kasa da talakawa da masu arziki da sarakuna da dukkan masu ruwa da tsaki su kula da tattalin arziki.

“Tattalin arzikinmu shi ne tsaronmu, shi ne siyasarmu, kuma shi ne karfinmu na fada a ji a duniya.

“Idan muna wasa da kanmu a harkar tattalin arziki to wallahi muna wasa da rayuwarmu ne baki daya a cikin duniyar nan. Don haka ba za mu yi mutunci a wajen mutane ba a duniya kuma ba za mu yi kima ba a idon wasu kasashen” a cewar Dakta Isa.

Ga jerin wasu hanyoyi da kwararru irin su Dakta Isa da kuma Farfesa Sule-Kano ke ganin sun kamata a bi don kawo karshen matsalar rashin aikin yi.

1. A nada kwamitin kwararru na gida da waje da kungiyoyi da cibiyoyi masu zaman kansu da na gwamnati don tsara wata manufa ta gyara tattalin arziki.

2. A rage dogaro da man fetur a koma wa gona ka’in da na’in musamman noman zamani ta hanyar diban arzikin man fetur din a zuba jari a harkar noman.

3. A samar da tsari na adana da kuma na sarrafa kayan da za a dinga nomawa a zamanance.

4. A rage dogaro da shigar da kayayyaki daga kasashen waje.

5. Hukumomi su yi amfani da dumbin arzikin da ke jibge a karkashin kasa wajen kirkirar wa al’umma aikin yi bisa ka’ida ta hanyarsu.

6. A samar da na’urorin zamani na kimiyya da fasaha da za a dinga amfani da su wajen tonon arzikin kasa da sarrafa su, ta yadda miliyoyin mutane za su samu ayyukan yi.

7. A koma a gyara kura-kuran baya na yadda aka dinga rufe masana’antu da masaku kusan 500 a Nijeriya. A sake bude su ta yadda za a samar wa dumbin mutane aiki.

8. Gwamnati ta daina sayen tataccen man fetur daga kasashen waje bayan “mu muke sayar musu da danyen.” A gyara matatun mai ta yadda ‘yan kasa za su samu ayyukan yi sosai.

9. Fadada da gyara harkar ilimi na zamani sosai mai cike da koyar da dabaru wanda zai bai wa ‘yan kasa damar lalubo bakin zaren magance matsalolin rashin aikin yi da kansu.

10. Sanya kudi a fannin kere-kere da yin abubuwan da kasar za ta iya fitarwa kasashen waje don habaka tattalin arziki.

11. Kawar da cin hanci da almubazzaranci da kudaden gwamnati, lamarin da ke dakile kokarin gwamnati na kirkirar damarmakin aiki.

12. Gwamnatoci a Nijeriya na bukatar kara kaimi wajen samar da yanayi mai kyau da kananan da matsakaitan sana’o’i da masana’antu za su bunkasa ta yadda dumbin mutane za su samu ayyuka.

13. A inganta samar da wutar lantarki don habakar kasuwanci.

14. Matasa su dinga amfani da basira da kwazonsu wajen zakulo dabarun fara kasuwanci ko wasu sana’o’i da za su dogara da su har ma su dauki wasu aiki.

15. Matasa su rage burin cewa sai aiki mai tsoka na ofis tare da rage raina fara sana'a komai kankantarta.

TRT Afrika