Kungiyar Missing Child Kenya na samun rahoton bacewar yaro a kusan kullum a Kenya. / Hoto: Others

Daga Sylvia Chebet

A lokacin da zuciyar Lynette Owande ta motsa - karar wayarta ce da aka saba kiran ta da ita, makociyarta ce tana magana cikin karkarwa, kuma zuciyarta na raya mata labarai.

Ya faru a ranar Talata a 2016. Yaronta mai shekara uku a wannan lokacin, Randall Osteen, ya bata ko kuma an yi garkuwa da shi a gidansu da ke Rongai, wani karamin yanki a wajen babban birnin Nairobi.

Wadda ake zargi da garkuwa sabuwar mai aiki da aka dauka a gidan su yaron ce, mace matashiya da duka kwananta biyu kawai a gidan.

A rana ta uku, da misalin karfe 4 na yamma, makociyarta ta yi zargin akwai wata babbar matsala, a lokacin da yaranmu biyu maza da ke wasa a harabar gidansu ba su zo sun ci abinci ba," kamar yadda Lynette ta fada wa TRT Afrika.

A yayin da makociyarta tata ta fita waje cikin alhini don duba me ke faruwa, sai ta ga kofar a bude, kofar baya ma an bude ta, kuma an jefar da kayan sawa na yaron a ko’ina. Sunan yaron Chichi, ba ya nan, haka ma mai kula da gidan ba ta nan.

“Ina wajen aiki a lokacin da ta kira ni a waya. Na kira mijina, sai muka tafi ofishin ‘yan sanda mafi kusa tare da bayar da rahoto kan batan yaron”.

Kara sanya idanu

Missing Child Kenya, wata kungiyar aiki kyauta da aka samar shekaru shida da suka wuce, ta taimaka wa jami’an tsaron Sashen Binciken Manyan Laifuka neman Randall ta hanyar yada kalmar ta shafukan sada zumunta.

“Cikin awanni, sai muka fara samun kira da sakonni daga ko’ina. Washe gari da misalin karfe uku na rana, sai muka samu labarin an gano inda yarinyar ta je ta buya a yankin Kiseria. Na samu sauki saboda an kubutar da yarona.”

An daure mai garkuwar da abokan aikinta na tsawon shekara guda a gidan kurkuku.

Da a ce ba a yi sanarwar batun garkuwar ba, da labarin Chichi ya zama wani na daban.

Missing Child Kenya da Sashen Binciken Manyan Laifuka sun hada kai da Meta don samar da ‘Sanarwar Amber” a Kenya, wata fasahar da za ta kawo sauyi a fannin nema da kubutar da yaran da suka bata ko aka sace.

“Damar neman yaran da suka bata ta karu sosai a yayin da mutane da dama ke ci gaba da duba, musamman awanni kadan bayan da aka rawaito wannan labari,” in ji Maryana Munyendo, daya daga cikin wadanda suka samar da Missing Child Kenya.

“Awanni 48 na farko na da matukar muhimmanci saboda suna dauke da muhimman shaidar batan yara. Misali, idan kana neman yaron da yake sanye da jajayen kaya, ko wani da aka gani a karon karshe a tashar mota kaza, yada wannan bayani zai bayar da dama a nemo su cikin sauri da sauki.

Tagwayen turakun kubutar da yara

Missing Child Kenya na amfani da karfin da jama’a ke da shi, kamar yadda kuma fasahar kere-kere ke da muhimmanci a wajen su. "Su ne idanuwanmu" in ji Munyendo.

Kaddamar da Sanarwar Amber ta kawo sauyi sosai a Kenya, wanda ya zama abin da ake wa lakabi da "Sanarwar Gaggawa Ta Kenya Game da Yara".

"Hukumomin tsaro sun kaddamar da Amber. A Kenya, abokan huldarmu su ne Sashen Bincikn Aikata Manyan Laifuka. Idan kana yankin da ake neman wani a wajen, sanarwar za ta bayyana shafinka na Facebook da Instagram," in ji Munyendo.

Hakan na nufin idan yaro ya bata a Nairobi kuma mai amfani da shafin sada zumunta na da nisan tsakanin kilomita 100 zuwa 160 a yankin da ake neman yaron, to mutum zai samu sako kai tsaye game da batan yaron ta shafin Facebook ko Instagram

Sanarwar da za ta zo za ta kunshi muhimman bayanai game da batan yara, tare da hoto mai kyau tare da dan gajeren bayani, adireshin gida, makaranta, da kuma idan zai yiwu a bayar da hoton wanda ake zargi .

Wasu sauran bayanai masu muhimmanci sun hada da me yaron da ya bata yake sanye da shi a karon karshe, a ina ka gan shi, shi yana da wata matsala ta lafiya ko tawaya?

"Suna bayyana cewa sai kauye sun hadu suke rainon yaro. Sannan sai jama'ar kauyen sun taru za su kare wannan yaron." in ji Munyendo. "Idan muka hada kai tare da yin kokarin da ya dace, za mu iya rage yawan lokacin da ake dauke na dawo da yaran da suka bata zuwa ga iyalansu."

Ga iyaye masu godiya irin su Lynette, suna kallon wannan aiki a matsayin abu ne daga Ubangiji.

Ta fada wa TRT Afirka cewa "Ban taba samun farin ciki irin haka ba kamar na lokacin da aka gano yarona. Na san Ubangiji zai kawo mana dauki, amma farin cikin sake rungumarsa wani abu ne da ba zan iya fayyacewa ba. Ina godiya ga Allah saboda wannan abin ta'ajibi."

Yaki da fataucin mutane

Kenya ce kasa ta hudu a Afrka da ta fara aiki da sanarwar Amber, an bai wa tsarin sunan yaron da aka yi garkuwa da shi a Amurka. Wasu da suka yi amfani da shi sun hada da Afirka ta Kudu, Morocco da Nijeriya, inda aka yi garkuwa da sama da yara 1,400.

Missing Child Kenya na samun rahoton batan yara 30 a kowanne wata. Daga cikin yara 1,551 da ta bibiya tun bayan kaddamar da su a Kenya, kungiyar ta kubutar da yara 1,208. Har yanzu tana ci gaba da neman wasu 315, inda 28 suka mutu.

Tsawon shekaru, kungiyar ta fahimci sauyi. Wahalhalun tattalin arziki na daya daga cikin manyan dalilan da ke sanya yara su bata.

"Muna samun rahotanni dayawa daga birane da ma kauyuka saboda yara na fuskantar kalubalen wahalar rayuwa, ciki har da rashin samun ilimi mai kyau, da kuma rashin kyakkyawar kulawa daga iyaye." in ji Munyendo.

Irin wadannan yaran na fadawa mummunan yanayi ko hannun masu garkuwa da mutane da ke jan ra'ayin yara ga ingantacciyar rayuwa.

Wani batun kuma shi ne al'ada. Rashin haihuwa na bayar da gudunmawa wajen batan yara kanana, saboda na kokarin satar yara da su kubutar da aurensu. Haka ma matsafa na bayar da gudunmowa wajen batan yara kanana.

Abu ne da aka saba gani yara kanana su fita gararamba a kan tituna a lokacin da suke dawowa gida, amma kwararru kan kare yara sun ce wadannan hanyoyin da yara suka fi bata.

Sai dai kuma, yaran da suka kai shekara biyar da kuma masu bukata ta musamman ne suka fi fadawa wannan hatsari.

TRT Afrika