Abu na karshe shi ne akwai bukatar sana'anta gishirin ya kasance an bi ka'idojin da suka dace.

Daga Firmain Eric Mbadinga

Gishiri mai dandano. Babu abincin da dandanonsa zai cika ba tare da gishiri ba. Hakan ya sa yake da matukar muhimmanci ga dukkan girki.

Kai ka ce sihiri ne, amma a zahiri gishiri yake canja dandanon abinci, inda yake mayar da abincin mai dadi.

Domin jin dadin dandano ba tare da illa ga lafiya ba, Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta ba da shawarar kar manya su ci sama da giram biyar na gishiri a kullum. Sannan kananan yara kuma masu shekara tsakanin biyu zuwa biyar kar ya kai haka. Sannan ta ce dole ya kasance gishirin yana dauke da sinadarin iodine domin kula da ingancin lafiya.

Abu na karshe shi ne akwai bukatar sana'anta gishirin ya kasance an bi ka'idojin da suka dace.

Inganta tattalin arzikin mutane

A kasar Senegal, yankin Fatick da ke yankin tsakiyar kasar da Sédhiou da ke Gabashin kasar sun mayar da sana'anta gishirin tamkar wata sana'ar al'ada domin inganta tattalin arzikinzu. Sannan yawancin wadanda suke aikin gishirin mata ne.

A shekara hudu da suka gabata, Univers-Sel ta fi mayar da hankali ne a kan ayyuka biyu da za su inganta sana'ar ga mata.

Louise Laroye, shugaban samar da ci gaba na Kungiyar Univers-Sel ya dade yana ayyukan inganta sana'ar yin gishiri a garin Palmarin da Djilasse da Loyal Sésséne dukkansu da suke kusa da teku a yankin Fatick.

Kungiyar Univers-Sel na aiki ne tare da kananan masu sana'ar domin zamanantar da harkar domin ya kasance gishirin da ake yi na da inganci, sannan bai konewa sosai a lokacin aikinsa.

A shekara hudu da suka gabata, Univers-Sel ta fi mayar da hankali ne a kan ayyuka biyu da za su inganta sana'ar ga mata.

"Muna da shirin Ndappe O Diem, wanda ke nufin rumbun gishiri a harshen Serer da muka fara a Oktoban 2022. Sannan akwai shirin Resilao, wanda yake a Palmarin, wanda shi ma aka fara a watan Fabrailun bana," inji Louise a tattaunawarsa da TRT Afrika.

Dukkan shirin suna karkashin Hukumar Kula da Cimaka da kasar ne, inda suke kokarin hada kan masu sana'anta gishiri a Senegal da wasu kasashen duniya.

"Ofishin da ana kiransa ne da suna Cellule de Lutte Contre la Malnutrition, wato sashen kula da cimaka, inda yake taimakon masu sana'anta abinci wajen yaki da rashin isasshen sinadarin iodine a abinci. Da farkon, sashen ya sha fama wajen samun hadin kan masu aikin gishiri. Wannan ya sa suka neme mu," inji Louise.

Bincikenmu ne ya sa muka assasa wani shiri a shekarar 2020 da muka sa wa suna APEFASS. Daga baya kuma muka assasa shirin Ndappe O Diem.

Yanzu ramukan aikin gishirin sun fara maye gurbin wadanda ake amfani da su a da.

Tuna baya

Gishiri shi ne kusan kashi 3.5 na tekunan da muke da su a duniya. Haka Allah Ya ke halittarsa a lokacin da aka tare ruwan teku, sannan aka busar da shi da wuta ko zafin rana, sai ya zama gishiri.

Haka za a cigaba da gasawa har sai sinadarin sodium chloride ya fita baki daya daga ramin. Daga nan sai a tace, a karasa sana'anta gishirin kamar yadda ake so.

A shekaru da dama da suka gabata, kananan masu sana'ar sun yi amfani da hanyoyi daban-daban wajen aikin gishirin. A kasashen Guinea-Bissau, Gambia, Niger da Senegal, sun fi amfani da zafin rana wajen busar da gishirin.

Serra Salt Machinery, wani babban kamfani ne a duniya da ya fi kwarewa wajen aikin kimiyya da gine-gibe, da hada kayayyakin aikin gishiri, ya yi bayanin cewa amfani da zafin rana shi ne tsohon hanyar busar da gishirin.

Hadi a kan wannan tsarin, ana kuma amfani da itace wajen kona ruwan da ke cikin domin busar da gishirin.

Masana a bangaren suna cewa wannan tsarin ana kona wasu ababe irin su itace, wadanda suna da illa ga muhalli.

Hanya mafi kyau

"Ba ma amfani da wannan tsarin," in ji Louise.

"Tsarin da muka fi amfani da shi a Senegal, musamman a wuraren da muke aikin, yana bambanta da na Casamance da ma Guinea-Bissau. A nan, muna amfani da ramukan gishiri me. Ba ma bukatar kona itace."

Univers-Sel tana kokarin hakan ne domin hana daidaikun masu sana'ar yanke bishiyoyi da kona su.

Louise Demba Sarr, Tsohuwar Shugaban Kungiyar Masu Sana'ar Gishiri na Palmarin, tana cikin wadanda suka ci moriyar kungiyar.

"Mun dade muna wayar da kan mutane a kan wannan tsarin. Muna jin dadin aiki da rana da iska. Muna samun ingantaccen gishiri a duk lokacin rani, wato tsakanin Janairu da Mayu," inji Emmanuel Deniaud, daraktan kungiyar.

Louise Demba Sarr, Tsohuwar Shugaban Kungiyar Masu Sana'ar Gishiri na Palmarin, tana cikin wadanda suka ci moriyar kungiyar.

"A da can ba mu cika damuwa da Ingancin gishirin ba. Amma da taimakon Kungiyar Univers-Sel, mun samu karin ilimi domin inganta aikinmu. A da can, mukan cakuda gishirin da muka hada na farkon da na biyu da na uku a waje daya, alhali na karshen bai cika kyau ba," kamar yadda Sarr ta bayyana wa TRT Afrika.

Ta bayyana cewa abokan aikinta ma suna ka kokarin fadada iliminsu domin inganta sana'ar. "Duk shekara, mutane Kungiyar Univers-Sel suna taimaka mana wajen shirya mana tarukan kara ilimi."

Kula da sana'anta gishirin da amfani da shi

Da taimakon Kungiyar Univers-Sel, Gwamantin Senegal ta mayar da hankali wajen ganin kananan masu aikin gishirin sun samu ilimin da ake bukata domin ganin sun samar da gishiri mai isasshen sinadarin sodium, sannan suna aikin ne ba tare da sun illata muhalli ba.

Duk da cewa sinadarin sodium yana da amfani a jikin mutane domin daidaita ruwan da ke jikin mutum, da daidaita yanayin gubar asid da ke jikin mutum da kuma kula ayyukan bangarorin jiki, idan ya yi yawa kuma yana jawo hawan jini da kansa da cutar kiba da sauransu.

Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta kiyasta cewa ana samun akalla mutuwa miliyan 1.89 da suke da alaka da sinadarin sodium.

Kamar yadda kididdigar ta nuna, a yankin Afrika ta Yamma, Senegal ce kan gaba wajen samar da gishiri, inda ake sana'anta tan 450,000 duk shekara, kusan tan 150,000 ke nan sama da makwabciyarta Guinea-Bissau.

Wannan ma wata nasara ce kasancewar Afirka na shigo da gishiri domin samun tan 7,000,000 da UNICEF ta ayyana ana bukata duk shekara.

TRT Afrika