Iya rubutu da karatu a tsakanin yaran gabashin Kongo na kasa da na yaran sauran yankunan kasar. Hoto: UNICEF

Daga Kudra Maliro

Suna karkashin tantunan da suka zama azuzuwansu, Rufin Kambale na koyar da darasin sanin taswira ga 'yan aji huɗu a makarantar Firamare ta Sayo, ɗaya daga cikin irin waɗannan makarantu da ke cikin mummunan yanayi a lardin Arewacin Kivu da aka raba da rikici a Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo.

A ƙarƙashin zafin rana ko a lokacin da ake mamakon ruwan sama, waɗannan tantuna da UNICEF ta samar ba sa isa a zauna a yi karatu.

Hudojin da ke saman tantunan na sanya hasken rana da ƙura shiga ajujuwan kai-tsaye. Wataƙila yaran masu tasowa da neman ilimi sun saba da wannan yanayi, amma malamarsu na kallon yadda suke ƙoƙarin sabawa da wannan hali.

"Yana da wahala yara su halarci darasi a cikin irin wannan yanayi mara kyau. Ba kawai sakamakon da suke samu ne yake raguwa ba, suna ma kasancewa a baya sosai a tsarin manhajar koyarwa ta kasar," Rufin ta shaida wa TRT Afrika.

Babu shaidar sakamako

An ɗauke makarantar daga Sayo, gari mai nisan kilomita 10 daga garin Beni, don kare ta daga harin 'yan bindiga na Allied Decratic Forced (ADF).

Makarantu da dama a yankin da ake rikici sun ci gaba da zama a rufe, hakan na tirsasa wa ɗalibai zama a gida ko yin wasu 'yan ayyuka don samun 'yan kuɗaɗe.

"Tun bayan harin da aka kai wa ƙauyenmu a 2016 na ke zaune a gida ba batun zuwa makaranta," in ji Josian mai shekara 24.

Hukumar UNICEF ta bayyana cewa 'yan tawaye da ke kai hare-hare sun raba kusan yara kanana miliyan ɗaya da matsugunansu a Arewaci da Kudancin Kivu.

Josias, kamar sauran matasa da suka guje wa hare-haren ADF a yankin Beni, yana neman mafaka a wajen shan ƙwaya a duk lokacin da ya rasa yadda zai yi.

A wasu lokutan, yana sayar da takalma don ya rayu, ya manta da burinsa na son zama likita.

Duk sakamakon kammala zangon karatunsa sun ƙone a lokacin da aka yi wata gobara bayan an kai wa ƙauyensu hari.

Rikici a gabashin Jumhuriyar Dimokuradiyyar Kongo ya raba yara kusan miliyan guda ma matsugunansu, kamar yadda MDD ta bayyana. Hoto: UNICEF

Kukan neman taimako

Halin da zuciyar Josias ke ciki na bayyana irin na yara da suke makaranta kuma aka raba su da matsugunansu.

Esdras Kambasu, shugabar makarantar Firamare ta 'Ecole Primaire D'application' da ke Beni, ya yi nuni da cewa mafi yawan daliban ma na ɗimauta a azuzuwa. Zai so ya ga wani tsarin taimakawa na musamman ga wadannan yara.

Ya fada wa TRT Afirka cewa "Yaran da ake raba wa da matsugunansu na bin sahun sauran dalibai. Suna amfana da samun ilimi kyauta, kuma ana barin su a baya a manhajar ilimi ta kasa.

Domin kamo sauran, iyaye na iya biyan malamai su baiwa yaransu darashi na musamman.

A yayin ziyara zuwa DRC, Volker Turk, Babban jami'in Majalisar Dinkin Duniya Mai Kula da 'Yan Gudun Hijira, ya ce ya zama dole kasashen duniya su farka game da rikicin na gabashin kasar.

Kusan mutum 300,000 ne suka gudu zuwa garin Goma da yankunan da ke kewaye da shi. A yayinda ake ci gaba da rangama, ayyukan jinkai sun munana, na kara ta'azzara halin da mutum miliyan 7.2 da aka raba da matsugunansu ke ciki.

Farautar 'yan tawaye

"Za mu ci gaba da kira da a kare hakkokin ɗan'adam musamman hakkokin wadanda aka raba da matsugunansu," in ji Turk.

Masu koyo da dama na zuwa azuzuwa, suna smaun litattafai kuma ga wuraren zama. Hoto: UNICEF

Rashin samun isasshen abinci na nufin yara za su zo makaranta suna jin yunwa. Wasu mugaye ne kawai suke hana a gudanar da ayyukan jinƙai a yankin.

Rashin tsaron ya raba malamai da dama da matsugunansu, suna gwagwarmaya kamar ta yaransu.

Gwamnatin Jumhuriyar Dimokuradiyyar Kongo ta sha zargin makociyarta Rwanda da goyon bayan 'yan tawayen, amma Kigali na musanta wannan zargi.

Kinshasa ma ta kawo karshen ayyukan Dakarun Gabashin Afirka, wadanda ta zarga da gaza magance matsalar 'yan tawayen.

A watan Disamban 2023, kasar ta nemi taimako daga Kungiyar Kasashen Kudancin Afirka "don taimaka wa gwamnakin Kongo a kokarin da take yi na dawo da zaman lafiya da tsaro a gabashin Jumhuriyar Dimokuradiyyar Kongo."

Fatan samun zaman lafiya

Wannan tawaga ta sojoji da ta ƙunshi dakarun Afirka ta Kudu, Malawi da Tanzania, sun je DRC don yakar 'yan tawaye, ciki har da M23, wadda ke kai hare-hare a gabashin kasar.

Duk da wannan rikici, masu koyo na ta fatan ganin sun koma makaranta. Hoto: UNICEF

Duk da hare-haren 'yan tawayen da wahalar rayuwa a sansanonin wadanda aka raba a matsugunansu a wajen garin Goma, yara da ke neman ilimi na fatan komawa azuzuwa kamar yadda suke zuwa makaranta a baya.

Rose Batumike, 'yan shekara 17 da ta rayu a sansanin Goma tun bayan guje wa harin M23 a Rutsuru, ba ta fitar da rai ba a cika burinta na komawa jami'a ta kammala digiri ba.

Matashiyar ta fada wa TRT Afirka cewa "ya kamata gwamnatin Kongo ta magance 'yan tawayen nan da nan ta yadda zan samu damar koma wa makaranta....ban san komai game da siyasa ba. Fatana kawai shi ne zaman lafiya ya dawo Jumhuriyar Dimokuradiyyar Kongo."

TRT Afrika