Diamond Platnumz  (Dama) an nada shi a matsayin mai neman kambin Mawakin Afirka Namiji Mafi Kwarewa a Afirka  Hoto: Diamond Platnumz 

Daga Charles Mgbolu

A yayin da watan Agusta ke dab da karewa, ana shirin shiga zangon 2023/2024, an kuma nada mawaka da dama da suka yi shuhura a fannoni daban-daban.

'Trace Music', wani dandalin wakoki ne na Afirka, ya kuma saki jerin sunayen mawakan da ke fafatawa don lashe gasar mawaka ta farko ta nahiyar, wadda za a gudanar a Kigali, babban birnin Rwanda a ranar 21 ga Oktoban 2023.

Akwai kambi 22 da ake jiran a lashe su, inda mawaka fitattu daga kasashen Afirka sama da talatin, Kudancin Amurka, Karibiyan, Tekun Indiya da Turai za su fafata da juna.

A bangaren gwarzon mawaki namiji, Nijeriya na da wakilci mai karfi daga Asake da Burna Boy da Davido da kuma Rema.

Last Last ta Burna Boy na daga wakokin da suke takara a bangaren Mawaka Mafiya Dadi. Hoto Burna Boy

Sai dai kuma, za a samu gogayya mai karfi daga Daimaond Platnumz (Tanzania), Didi B (Ivory Coast) da K.O. (Afirka ta Kudu).

A bangaren mawaka mata mafi shuhura da kwarewa akwai Ayra Starr (Nijeriya), Josey (Ivory Coast) da Nadia Mukami (Kenya), Soraja Ramos (Cape Verde), Tiwa Savage (Nijeriya) da Viviane Chdidi (Sanagal) za su fafata don neman lashe kambin.

Za a yi fafatawa mafi zafi ne a bangaren zabar 'wakar shekara', inda wakoki 12 za su fafata da juna.

Wakokin 'Last Last' ta Burna Boy da ya lashe gasar Grammy ma na jerin wadanda ke neman lashe wannan kambi, amma tana da 'yan hamayya irin su Calm Down ta Rema daga Nijeriya.

Sauran su ne wakokin 'Sugarcane' ta Camidoh (Gana), 'Peru' Fireboy DML (Nijeriya), Ed Sheeran (Ingila), 'BKBN' ta Soraia Ramos (Cape Verde), 'Encre' ta Emma'a (Gabon), 'Rush' ta Ayra Starr (Nijeriya) da kuma 'Cough' ta Kizz Daniel (Nijeriya) wanda suk za su fafata a gasar.

Nadia Mukami na sa ran lashe kambin mawakiya r Afirka. Hoto Nadia Mukami

Kamaru ma na da karfi a wannan gasa, ind amawaka biyu, Krys M. da Libianca za su fafata a bangaren mawaka sabbin jini.

Wadanda suka lashe kambi na gasar 'Trace' za su tafi gida da kyaututtukansu, wadanda abubuwa ne na musamman da aka samar. Dan kasar Kongo mai sana'ar sassaka Dora Prevpst ne ya samar da kambinan.

Shirya gasar lashe kambi ga mawakan Afirka na taka muhimmiyar rawa wajen fito da mawakan duniya ta san da su, sannan hakan na kara nuna kwarewar kida da waka a Afirka kamar irin salon Afrobeat, Dancehall, Hip Hop, Afro=pop, Mbalax, Amapiano, Zouk da Kizomba.