Joyce Ijeoma ta suma a yayin da take kokarin kafa tarihi na wacce ta fi dadewa tana yi wa mutane tausa ba tsayawa./ Hoto :Autres

Daga Pauline Odhiambo

Joyce Ijeoma ta yi kokarin kafa tarihi a Guinness World Record (GWR) na zama wacce ta fi yi wa mutane tausa mafi tsawo ba hutawa a duniya.

Ijeoma, wacce ta yada bidiyo kai-tsaye na kokarin nata, ta sare inda ta fadi lokacin da ta kai awa 50 da farawa, ba tare da ta kai awa 72 da ta yi niyyar yi tana tausar ba.

A wasu bidiyoyi da suka yadu a intanet, an ga yadda ta fadi ta suma yayin da wani mutum ya yi kanta da gudu don taimaka mata. Ta fara wannan kokari na kafa tarihi a ranar 1 ga watan Yuli.

A yanzu haka wani dan kasar Indonesia mai suna Alastair Galpin ne ke rike da kambin wanda ya fi dadewa yana yi wa mutane tausa a duniya inda ya shafe awa 25 da minti hudu yanayi a 2015 a Kudancin Kalimantan na Indonesia.

Mai yiwuwa kanbin ya koma hannun Ijeoma tun da ta wuce tsawon lokacin da mai rike da shi ya shafe. Sai dai har yanzu Guinness World Records ba su ce komai ba kan wannan kokari nata mai cike da wahala.

Joyce Ijeoma ta yi kokarin kafa tarihi na wacce ta fi dadewa tana tausa./Hoto: Others

An yi ta surutai kan kokarin nata na samun nasara, abin da ya kai ta ga sumewa. Mutane da yawa sun ce mutum na bukatar cikakkiyar nutsuwa a jiki da kwakwalwa kafin ya fara wannan aikin.

Kallon fina-finai

"Kowa zancenta kawai yake yi kuma duk hankula sun koma kanta. Ina fatan a yaba da kokarinta a ba ta kambin," kamar yadda Lola Mustapha, wata mai bin ayyukan GWR sau da kafa ta shaida wa TRT Afrika.

'Yan Nijeriya suna ta azarbabin kafa tarihi a Guinness World Record, tun da wata 'yar kasar Hilda Baci ta samu nasarar kafa wannan tarihi bayan ta dauki lokaci mafi tsawo tana yin girki a watan Mayu.

Samun nasarar Hilda ke da wuya sai sauran 'yan Nijeriya suka fara kokarin nuna tasu bajintar su ma. Chef Damilola Adeparusi, da aka fi sani da Chef Dammy ma ta fara tata gasar girkin a ranar Alhamis 11 ga watan Mayu inda ta ci gaba har Litinin 15 ga Mayu, in da ta dafa abinci fiye da nau'i 100 bayan shafe kwana hudu tana fama a kicin.

Matashiyar 'yar asalin Jihar Ekiti ta yi kokarin cika burinta na yin girki babu kakkautawa tsawon awa 120, sai dai Guiness World Record ba ta bayyana amincewa da wannan kokari ba har yanzu.

A yanzu Hilda Baci ke rike da kambun wacce ta fi kowa dadewa tana girki. Photo: Reuters

Bayan Dammy, sai kuma wani mai girkin dan Nijeriya Prince Temitope Adebayo, ya fara kokarin wuce tsawon lokacin da Dammy ta dauka, in da ya kuduri aniyar yin girki na tsawon awa 140.

Can sai ga wani mai wasan barkwanci Woli Arole kuma ya iso da nasa burin na samun kambun wanda ya fi kowa dadewa yana addu'a, in da ya yi shirin shafe awa 5000 yana hakan. Ya kira nasa shirin da suna 'prayerthon'

Dokokin

Adebiyi Isreal daga Jihar Ekiti ma ya bayyana aniyarsa ta kafa tarihi na wanda ya fi daukar tsawon lokaci yana kallon fina-finai.

Wanda ke rike da wannan kambun a yanzu haka shi ne Suresh Joachim daga kasar Canada, wanda ya shafe tsawon awa 121 da minti 18 yana kallon fina-finai babu tsaya a shekarar 2015.

Shi ma wani mai sana'ar fenti Oyinlola yana shirin zama gwani na wanda ya fi daukar tsawon lokaci yana yin fenti don shiga kundin GWR.

A yanzu haka mai dauke da wannan kambu shi ne Ronald Palmaerts, wanda ya shafe tsawon awa 60 yana fenti babu tsayawa a shekarar 2013.

Sannan kuma Sultan “Hack Sultan” Akintunde, wanda yana daya daga cikin wadanda suka samar da makarantar AltSchool Africa ya sha alwashin zama wanda ya fi kowa dadewa yana nazarin dabarun manhaja.

Ya bayyana labarin hakan ne a shafinsa na Twitter, yana mai gode wa GWR kan damar da suka ba shi.

Wannan azarbabi na 'yan Nijeriya ya jawo cece-kuce sosai tare da jan hankali.

An yi ta murna kan kokarin da Hilda Baci ta nuna da kuma nasararta ta shiga kundin GWR. Photo: Reuters

Wasu na cewa lamarin ya zama wata gasa a kasar ga matasa da ke kokarin samun kambu da kafa tarihin yin wani abu da ya shafi zamantakewarsu. Amma wasu kuwa cewa suke yi, azarbabin ya fito da ainihin halayyar 'yan kasar masu kyau ne.

"'Yan Nijeriya da dama suna da kwarin gwiwa. Mun yi yarda da kawunanmu sosai. Don haka ba abin mamaki ba ne don muna kokarin kafa tarihi," a cewar Lola.

A cewar shafin intanet na GWR, dole sai mutum ya fara shiga rumbun bayanai na irin abubuwan da aka taba kafa tarihi a kansu kafin a fara kowane kokari.

'A jininmu abin yake'

Mataki na gaba shi ne sai a zabi fannin da ake son kafa tarihi, a nemi izinin farawa tare da jiran matakai. Da zarar an fahimci matakan, sai a fara.

"Ana bukatar lokaci sosai da sadaukarwa don zama mafi kwarewa a duniya," a cewar wata sanarwa da aka wallafa a shafin intanet din GWR. "Sai ka hau mataki na gaba sannan za ka fahimci ko za ka iya kafa tarihin duniya.

Fara kokarin kafa tarihin shi ne mataki na gaba. Bayan kammala wannan kuma sai a tafi mataki na karshe wato aika hukkar cewa an aiwatar da hakan ga alkalan GWR.

Ya kan dauki jami'an GWR wata uku kafin su yanke shawara kan wannan kokari, inda a mafi yawancin lokuta ake yin watsi da fiye da kashi 50 cikin 100 na ayyukan da ake aikawa saboda rashin isassun hujjoji.

Masu sa ido sun ce a yayain da ake ci gaba da azarbabin shiga wannan kudin, to ya kamata 'yan Nijeriya da sauran da ke burin kafa tarihi su dinga shirya wa shiga aikin sosai.

Lola ya yi imani cewa suman da Ijeoma ta yi watakila ba zai tsayar da azarbabin da mutane ke yi ba. "Burin son kafa tarihi da son zama gwanaye a cikin jininmu yake,'' ya ce

TRT Afrika