Kura-kurai biyar da mutane ke yi a ƙoƙarin kula da tsaftar bakinsu

Kura-kurai biyar da mutane ke yi a ƙoƙarin kula da tsaftar bakinsu

Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta ce kusan mutum biliyan 3.5 ne ka fama da matsalolin haƙori a duniya.
Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta ce kusan mutum biliyan 3.5 ne ka fama da matsalolin haƙori a duniya. /Hoto: TRT Afrika

Daga Sylvia Chebet

Warin baki da ciwon haƙori mai tsanani sakamakon ramukan da ke cikin haƙora na daga cikin manyan matsalolin da ke hana mutum sakat da yin rawar gaban hantsi.

Abin takaicin shi ne yadda wadannan matsalolin suka zama ruwan dare har ma suke jawo ruɓewar haƙora ko zubewarsu a wasu lokutan.

Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta ce kusan mutum biliyan 3.5 ne ka fama da matsalolin haƙori a duniya.

Sai dai a ƙoƙarin da wasu ke yi na gujewa ciwon haƙori ko warin bakin, wasu mutanen kan yawaita yin burosh ta hanyar dagewa da ƙarfi a yayin wanke bakin, lamarin da ke jawo ji wa haƙoran raunin da ka iya samar da rami a cikinsu, kenan an gudu ba a tsira ba.

Kura-kuran da mutane ke tafkawa a ƙoƙrin kula da tsaftar bakinsu na da matuƙar yawa, amma ga wasu biyar daga cikinsu:

Rashin yin buroshi yadda ya dace

Wataƙila a tunaninku saboda shekarun da kuka shafe kuna wanke haƙoranku ya isa a ce kun iya yin burosh yadda ya kamata ko? To mai yiwuwa ba haka ba ne, musamman la’akari da cewa wasu mutanen sun ɗauki batun wanke baki tamkar wata al''ada da suka taso da ita kawai.

Da take magana da TRT Afirka, Dr Radhia Okumu wacce kusan a kullum tana ganin ɗumbin marasa lafiya da ke fama da ciwon haƙori a asibitinta da ke Nairobi, ta ce "mafi yawanmu, mukan yi burosh, amma fa ba mu san ainihin yadda ake burosh ba."

Dirje haƙoran da burushi ta gaba da ta baya ba shi ne salon yadda ake wanke bakin ba a cewa ƙwararru, don kuwa dattin da ke maƙalewa ba ya fita ta hakan, musamman ta tsakanin dasashi.

Likitocin haƙora sun bayar da shawarar cewa danna buroshin da kyau a kan dasashi don cire datti ka iya jawo wata cutar haƙorin.

Daya daga cikin manyan kura-kuran da muke yi a lokacin yin burosh shi ne saka ƙarfi sosai. Don haka danna burosh din da ƙarfi a yayin wanke haƙora na iya jawo wata matsalar mai girma.

Dr Okumu ta ce mafi yawan mutane na tunanin yin hakan tamkar shi zai sa haƙoran su wanku da kyau, amma a zahiri illa suke jawowa haƙori da dasashi.

"Yana lalata haƙori saboda ya kawar da wasu sinadarai masu ba da kariya. Don haka a ƙarshe sai ya jawo ramuka a haƙoran."

Bayan haƙora, yana da muhimmanci a goge harshe. Hakan yana magance abin da ake kira halitosis (wato mummunan warin baki), lamarin da ke sa mutum jin kunya matsananciya, kuma alkaluma sun nuna cewa kashi 25% na al'ummar duniya na fama da shi.

“Har ila yau, ya kamata mu goge gefen kunci daga ciki. Shi ya sa muke maganar yin amfani da burushi mai laushi domin idan ba a yi amfani da irinsa ba, to hakan na nufin ba za a iya goge kunci ba.”

Kurkure baki bayan yin burosh

Bayan dirje bakin ciki da bai da ƙarfi da buroshi, abu na gaba da mutane da yawa suke yi shi ne kuskure bakin, har sai sun tabbatar babu sauran man goge bakin.

Ba zai yiwu a ce an iya wanke man goge bakin nan tas ba, dole a bar ɓurɓushi, don haka zai fi kyau a tofar maimakon a yi ta kurkure shi.

"Abin da ya kamata shi ne a kuskure baki kafin a fara burosh din, ta yadda idan an gama sai a tofar maimakon dagewa wajen ɗauraye bakin, don muna son wannan sinadarin fluoride da ke cikin man goge bakin ya zauna a bakinku."

Likitocin haƙori na son hakan don sinadarin fluoride din da za a bari a bakin zai ƙara ƙarfin haƙorin da kuma hana samar da rami.

Dr Okumu ta kuma ba da shawarar cewa idan har ana son amfani da sinadarin kuskure baki na kanti, to a bari sai aƙalla minti 30 bayan yin burosh.

Yin sakace kullum

Ƙwararru sun ce sakatar haƙori wani muhimmin abu ne na tsaftar baki da ke kawar da dattin da yake maƙalewa a tsakanin haƙora, kuma sau ɗaya ake son a yi shi a rana.

Rashin yin wannan al'ada yana ƙara yiwuwar gamuwa da matsalolin haƙori saboda ƙwayoyin bakteriya da ke yaɗuwa.

Ganin likitan zai taimaka wajen saurin ganowa idan har akwai wata matsala ta haƙori da ake dab da kamuwa da ita.: TRT Afrika

"Yawancin ramukan da muka saba fama da su, suna tsakanin hakora ne, ba a samu da yawa a haƙoran sama saboda ba laifi an fi kula da su, amma ba mu cika sakace tsakankanin haƙora da kyau ba," in ji Dokta Okumu.

Amfani da burosh yana goge kashi 60% na dattin, shi kuwa sakace yana goge kashi 40 na dattin.

Sai dai wasu mutanen sun fi son amfani da sinadarin wanke baki maimakon abin sakace na musamman da ba tsinke ba.

Amma dai wanke baki da burosh da kuma sakace ne kawai ke iya wannan aikin.

Abinci mai zaƙi da yawa

Yawan sukari yana lalata hakora musamman idan ba a wanke su ba da zarar an gama cin abu sai zaƙin. Shan ruwa nan da nan bayan gama cin zaƙi zai iya taimakawa wajen wanke sukarin.

Sannan abinci masu zaƙi sosai kan lalata haƙora da saka su saurin ruɓewa/

A lokacin kullen annobar korona, shan nau'in lemn tsami ya zama ruwan dare, ta yadda har likitocin haƙori suka dinga gargaɗi kan rage yawan sha.

Dr. Okumu ta yi gargadi. Ta ba da shawarar cewa idan dole ne a sha ruwan lemon tsami a kullum, to a yi amfani da abin zuƙa don guje wa haɗuwar lemon da hakora.

Likitoci kuma sun ba da shawarar cewa mutane su dinga shan ruwa da yawa. Da zarar bakinka yana jiƙuwa da ruwa sosai, to ba za ka dinga samun kogo da yawa a haƙoranka ba.

"A gaskiya yana da matukar muhimmanci saboda yana wanke ɓurɓashin abinci a cikin baki."

Ta kuma ba da shawarar cin cukwi don yana taimakawa wajen kwararar yawu da zagayensa a ciin baki sosai.

Sannan likitoci sun ce idan har ana son samun lafiyar haƙora sosai to ya kamata a guji shan sigari.

"Shan taba yana da illa ga lafiyarku.

Rashin zuwa ganin likitan haƙori

Wataƙila a ganinku don kuna wanke baki da yin sakace kullum sannan ba ku da wata matsala ta haƙori to ba sai kun je wajen likita ba ko?

Duk da haka yana da kyau sosai a dinga ganin likitan haƙori ko da sau ɗaya ne a shekara.

Ganin likitan zai taimaka wajen saurin ganowa idan har akwai wata matsala ta haƙori da ake dab da kamuwa da ita.

Abu mafi muhimmanci shi ne a sani cewa rigakafi ya fi magani, don haka kula da lafiyar haƙori abu ne mai kyau sosai.

TRT Afrika