Masana'antar shirya fina-finai ba masu shirya fim na cikin gida kawai suke da su ba, a yanzu ana samun masu dukar nauyin yada fina-finan a ma shirya su: Hoto/Reuters

Daga Abdulwasiu Hassan

Manhajojin nuna fina-finai suna zazzafar gasa da rige-rigen jan hankalin masu kallo a Nijeriya, lamarin da ke yin tasiri wajen sauya yadda ake kallon fina-finai a gidaje, a kasar da masana'antar fina-finanta ce ta biyu mafi girma a duniya.

Manyan manhajoji irin su Netflix da Amazon Prime na kutsawa cikin masana'antar samar da fina-finan kasar a daidai lokacin da 'yan fim ke kokarin samar wa kansu wani matsayi a fannin.

Yadda 'yan Nijeriya suke bin wannan yayin na tururuwa zuwa wadannan manhajojin na kara karfinsu a kan harkokin nishadi da na kasuwanci na fannin.

"Manhajojin kallon fim a yanzu suna tasiri a kusan kowane abu da ya shafi harkar fina-finai a Nijeriya - ba a kallon da rarrabawar ba kawai," in ji Muhsin Ibrahim, malami a Jami'ar Cologne ta Jamus a hirarsa da TRT Afrika.

A yanzu yawan tattaunawa sosai a kan sababbin fina-finan da aka saka a shafukan sada zumunta. A ko yaushe idan aka saki sabon fim a Nijeriya a kan manyan manhajojin kasa da kasa, daga furodusoshin har 'yan kallon kan kai batun soshiyal midiya a yi ta muhawara a kai.

Shaharar lamarin a intanet na kara sa wa mutane zakuwar son ganin fim din da kusan kowa ke magana a kai. Hakan nasarar dukkan manhajojin ne a wajen bunkasarsu.

Girman tasirinsu

Masana'antar fim din Nijeriya wata masana'anta ce mai fitar da fina-finai tamkar masana'antar Hollywood

Masu shirya fina-finan Nijeriya na fatan janyo hankalin manhajojin kasa da kasa zuwa ga fina-finan kasar: Hoto/Reuters

Sunan masana'antar Nollywood, amma akwai rabe-rabenta kamar Kannywood na Hausa da Yollywood na Yarbanci. Kannywood ya samo asalin sunansa ne daga Kano, inda can ne cibiyar shirya fina-finan Hausa. Yollywood kuma ya samo asali daga Yarabanci.

Duk da cewa sauyin da ake samu wajen yada fina-finai da kuma kallon fina-finai yana sauya abubuwa a masana'antar, babu tabbacin iyakar sauyin.

Muhsin ya ce yayin komawa kallon fim ta intanet ya jawo durkushewar tsarin kallon fim ta hanyar sayar da shi a kaset da aka saba yi a baya. "Tuni daya daga cikin manyan masu irin wannan kasuwancin na sayar da fina-finai ya rufe shagonsa. Wannan salo na ta kwashe masu kallo zuwa manhajojin yanar gizo."

Amma a ra'ayin Ishaya Bako, mai sana'ar shirya fina-finai a Nijeriya, wannan salo bai yi irin tasirin da mutane ke tunanin gani ba.

Ya ce "Duba ga yawan jama'armu, har yanzu manhajojin yanar gizo ba su da mabiya da yawa a Nijeriya."

Daraktan da shirin sa na '4th Republic' ke jerin fina-finan da suka yi shuhura a Nijeriya kuma ake nuna su a Netflix a yanzu haka, ya yi nuni da cewa har yanzu mutane na amfani da faya-fayan garmaho a kananan biranen kasar.

Karbuwar da manhajojin nuna fina-finai ke samu na yin illa ga rarraba fina-finan a faya-fayan garmaho manyan da kanana: Hoto/Reuters

Lokuta masu armashi

A lokaci guda, Bako ya gamsu da cewa kirkirar manhajojin yanar gizo ya samar da kyakkyawar dama ga 'yan Nijeriya da ke da fasahar shirya fina-finai.

"Lokaci ne mai faranta rai ga al'adunmu. Ana yada al'adun Afirka a wajen nahiyar, ana nuna al'adun ga duniya a manhajoji kamar su Netflix, Amazon Prime Disney Plus da Showmax, wanda ke ta kokarin tabuka katabus a kasuwannin Afirka," in ji shi.

Wani babban kalubale shi ne tsadar rayuwa a Nijeriya a yau, wanda zai sanya da wahala mutane da dama su samu ikon biyan kudaden wata-wata na wadannan manhajoji, musamman na kasa da kasa.

Northflix na mayar da hankali kan fina-finan arewacin Nijeriya, wanda ba a nuna su a kan manhajojin kasashen waje.

Shugaban Northflix Jamil Hajaj, na da ra'ayin wannan kamfani na da makoma mai kyau, duba da yawan masu magana da yaren Hausa a yau a duniya.

Ya fada wa TRT Afirka cewa "Na yi amanna muna da masu magana da Hausa sama da miliyan 120. Mun mayar da hankali ne a kansu."

Northflix na kara samun karbuwa a Kannywood: Hoto/Facebook/Northflix

Matsalar satar mallaka

Tsofaffin hanyoyin yada fina-finai na faya-fayen garmaho na bayar da damar a sace su a sake sarrafa su.

Da zarar an saki wani shirin fim, nan da sai ka ga kwafinsa da aka sata aka sake buga shi ya cika kasuwanni da shaguna, wanda hakan ke dakusar da masu shirya fina-finai.

Wasu sun yi fatan cewa nuna fina-finansu a shafukan yanar gizo wajen samu masu kallo da yawa, kuma hakan zai sanya a magance matsalar satar fina-finan ana sake buga su, amma kuma sai ga shi wannan matsala ta ci gaba.

A shafukan sada zumunta wani mai shirya fina-finai da ya saki sabon fim a kan manhajar ya yada hoton wani mutum da aka kama da kwafin sata na fim dinsa. Ba a gama gano ko an nadi shirin fim din daga manhajar ne a yayin da ake kallo ba.

Northflix ya jaddada lallai manhajarsa ba ta damar a saci fina-finan da ke kan ta. "irin tsarin tsaro da muka yi amfani da shi wajen hada wannan manhajar ba ya bayar da dama a kwafi wani abu ko a sauke shi," in ji Hajaj.

Na gida da na waje

Ya zuwa yanzu, manhajojin cikin gida a Nijeriya ba su fara nuna fina-finan Kannywood ba, wanda abu ne da Nortflix ke ribata.

Northflix na cajin Naira 1,000 (dala 1.3) don sayen kallon a matakin farko, hakan ya zo ne duba da nazarin da suka yi kan karfin aljihun masu kallo.

Wasu masu nazari na ganin nuna fina-finai a manhajojin gida ba za su iya gogayya da na kasa da kasa ba: Hoto/Facebook/Northflix

Hajaj ya bayyana cewa manhajar ta samu mabiya da dama da suke iya biyan kudi daga wuraren da bai taba tunanin akwai masu magana d ayaren Hausa ba.

Ya ce "Manufarmu ita ce mu samu mabiya miliyan daya. Idan kana da mabiya miliyan daya, kowa na biyan Naira dubu daya, wannan adadin kudi ne mai yawa. Kana maganar kusan Naira biliyan daya ne a kowanne wata."

"Ka yi tunanin idan rabin wannan kudi ko kaso biyu cikin uku yana koma wa ga masana'antar fina-finan, abu ne da zai kawo sauyi."

A daya gefen kuma, ana da dimbin mabiya Netflix da Amazon Prime, d akuma yiwuwar a nan gaba wadannan manhajoji na kasa da kasa su fara nuna fina-finan Hausa.

Masu shirya fina-finai kamar Bako ba sa korafi. Matukar akwai masu bibiya da za su dinga kallo a manhajoji, to akwai dukkan dama ta shaida wa duniya hkayoyi daga Nijeriya da sauran yankunan Afirka.

TRT Afrika