Babban Zauren Majalisar Ɗinkin Duniya ya gudanar da taro na musamman kan Falasɗinu a hedikwatar majalisar da ke Birnin New York a ranar 10 ga watan Mayun 2024. / Hoto: AFP

Ƙuri'ar da Majalisar Ɗinkin Duniya ta yi a ranar Juma'a kan goyon bayan ko Falaɗinu ta zama ɗaya daga cikin mambobin ƙungiyar ya kasance lamari mai kyau amma kuma zaɓe ne na je ka na yi ka. Idan za a yi adalci, za a samu wasu alfanu dangane da hakan, amma shin wani abu zai sauya halin da ake ciki a yanzu?

Ƙuri'un da ƙasashe 143 suka yi na amincewa da Falasɗinu ta zama cikakkiyar mambar MDD, sun yarda ta zama cikakkiyar mambar MDD da kuma bayar da shawara kan ta kuma zama mambar Kwamitin Tsaro na Majalisar Ɗinkin Duniya.

A 2012, duk da yadda Amurka da Isra'ila suka tsaya kai da fata suka ƙi amincewa, Falasɗinu ta zama ƙasa wadda ke da ikon zama mamba a a majalisar.

Wannan ya ba Falasɗinu damar shiga ƙungiyoyin duniya da na ƙasa da ƙasa waɗanda suka haɗa da Kotun Hukunta Manyan Laifuka ta Duniya domin gabatar da ƙorafi kan abubuwa, misali, yadda Yahudawa ke kama wuri su zauna a Gaɓar Yamma da Kogin Jordan da kuma hare-haren sojoji a Gaɓar Yamma da Kogin Jordan da Gaza.

Sai dai kafin ƙasa ta zama cikakkiyar mamba ta Majalisar Ɗinkin Duniya, sai ƙasashe 15 waɗanda mambobin Kwamitin Tsaro na Majalisar Ɗinkin Duniya sun amince da hakan, inda ciki ƙasashe biyar na da karfin su hana ko su saka a yi.

Idan aka yi la'akari da abin da ya faru a watan da ya gabata, Amurka ta hau kujerar na-ƙi inda ta ƙi amincewa da Falasɗinu a matsayin ƙasa mai cikakken iko.

Duk da haka, ko babu amincewar kwamitin tsaro na majalisar domin ta zama cikakkiyar mamba, Falasɗinawan a halin yanzu suna da abubuwan da za su mora.

Falasɗinawa ba za su iya jefa ƙuri'a a Babban Zauren Majalisar Ɗinkin Duniya ba, haka kuma ba za su iya gabatar da ɗan takara ba a manyan hukumomin majalisar, kamar a kwamitin tsaro da na tattalin arziƙi.

Sai dai ƙungiyoyin da ke goyon bayan Falasɗinu na fargabar idan aka yi wani zaɓe na daban na a Babban Zauren Majalisar Ɗinkin Duniya za a iya yin ƙuri'a wadda za ta iya sakawa a zaɓi 'yan Falasɗinu don su samu Hukumar Kare Haƙƙin Bil'adama ta Majalisar Ɗinkin Duniya. Wannan za ta iya zama dama ga Falasɗinun ta shigar da ƙara kan take haƙƙin bil adama da Isra'ila take yi mata.

Me ke ƙunshe a cikin zaɓen?

Kasashe tara ne suka kada kuri'ar kin amincewa da kasancewar Falasdinu: Amurka, Isra'ila, Argentina, Jamhuriyar Czech, Micronesia, Nauru, Palau, Hungary, da Papua New Guinea. Kasashen Rasha, China, Indiya, Indonesia, Afirka ta Kudu, Faransa, Sifaniya, Belgium, da wasu kasashen gabashin Turai suka goyi bayan kudurin.

Duk da irin goyon bayan da Jamus ta nuna ga Isra'ila ta hanyar ba ta makamai masu guba, ta ƙi yarda ta yi ƙuri'a. inda ita ma Birtaniya ta bi bayanta da Canada da Sweden da wasu ƙasashe 21.

Ƙin jefa ƙuri'ar a maimakon nuna adawa, wata alama ce da ke nuna cewa waɗannan ƙasashen ba za su iya ci gaba da adawa da zaman Falasɗinu a matsain ƙasa mai cikakken iko ba. Fargabar tofin Allah tsine daga 'yan ƙasa da kuma watakila saboda nuna girmamawa ga manyan masu goyon bayan Amurka da Isra'ila - Birtaniya, Canada da Jamus sun ja da baya daga goyan bayan kudurin inda suka zaɓi su yi shiru.

Duk da haka, ko da Falasɗinu ta samu cikakkiyar amincewa domin zama mamba a Majalisar Dinkin Duniya, wannan bai canza komai ba. Ba a kan batun samun cikakken ikon Falasɗinu da ne kaɗai aka mayar da hankali a wurin zaɓen ba.

A lokacin da take kare ƙuri'unta, Mataimakin Jakadan Amurka Robert Wood ya yi iƙirarin cewa za a iya amincewa da Falasɗinu ne kaɗai idan ta tattauna da Isra'ila kai tsaye.

Amurka da Isra'ila sun san cewa babu irin wannan tattaunawar a kan teburi. Haka kuma ikirarin tattaunawar nan gaba ba komai ba ne illa yaudara.

Amurka ta samu dama ta shekaru talatin don tabbatar da an gudanar da irin wannan tattaunawar. Maimakon haka, gwamnatoci daban-daban sun haɗa kai da Isra'ila kuma sun yi watsi da batun tattaunawar da gangan.

A maimakon haka, sai Amurka ta biya Isra'ila lada ta hanyar sayar mata da makamai masu kyau da kuma ba ta goyon baya a duk shekara.

Sakamakon irin goyon bayan da Amurka da wasu ƙasashen yamma ke ba ta, Isra'ila ta sauya inda ta ƙwace wasu ƙarin wurare a Gaza.

Tun daga 1967 zuwa 2017, Isra'ila ta ƙwace kadada kusan 100,000 ta Falasɗinu, kamar yadda ƙungiyar Amnesty International ta bayyana.

Fiye da murabba'in mil 386 na filayen Falasɗinu da Isra'ila ta ƙwace ya mayar da ƙasar kashi hudu na abin da aka ware mata a shekarar 1948. A watan Maris din shekarar 2024 an kwace wa Falasɗinu kadada 800, sannan an ƙwace mata wani fili mai murabba'in mil 3.

A yayin kuri'ar da aka kada a makon da ya gabata a Majalisar Dinkin Duniya, jakadan Isra'ila Gilad Erdan, ya nuna kyama ga baki daya baya ga yin Allah wadai da dukkan kasashen da suka kada kuri'ar amincewa da kudurin.

Ya yayyaga yarjejeniya ta Majalisar Dinkin Duniya gaba daya a gaban mambobin a matsayin wani aiki na nuna rashin amincewa. Erdan ba zai manta da gaskiyar cewa ita ce Yarjejeniya ta Majalisar Ɗinkin Duniya da ya wulaƙanta ita ta ba Isra'ila ƙasa.

Babban abin ban mamaki shi ne mugun zarge-zargen da Erdan ya yi na cewa Majalisar Dinkin Duniya tana maraba da "yankin ta'addanci" a cikin sahunta. Idan har akwai wani dalili da zai sa duniya ta fahimci dalilin da ya sa babu zaman lafiya a yankin, za a iya samun hakan ne daga halin da wakilin Isra'ila a Majalisar Dinkin Duniya da ayyukan kisan kare dangi da Isra'ila ke yi na tsawon watanni bakwai a Gaza.

Falasɗinawa sun taru a daidai lokacin da masu ceto suke neman waɗanda suka maƙale a ƙarƙashin ɓaraguzai da wani gini da Isra'ila ta rusa ya danne a Nuseirat da ke Gaza a ranar 14 ga watan Mayun 2024. / Hoto: Reuters

Sifaniya da Ireland da ma wasu kasashen Tarayyar Turai da dama na shirin amincewa da Falasdinu a matsayin kasa a ranar 21 ga watan Mayu, a cewar jami'in kula da harkokin waje na EU, Josep Borrell. Da dama jama'a ba su san yadda hakan zai yi tasiri ba

Harin Oktoba

Abin da ake ganin ya ƙara lalata al'amura shi ne irin abin da ya faru a ranar 7 ga watan Oktoban 2023.

Bayan an gaza kammala duk wasu nau'in tattaunawa, sai Hamas ta kai har. Wannan aikin da alama ya sake farkar da mutane a cikin furcin "rushe mulkin mallaka." Wannan ya canza gaskiyar da ke ƙasa kuma ya fito da rashin adalcin da aka yi a tarihi wanda aka yi wa Falasɗinawa inda aka rinƙa nuna hakan ga jama'ar duniya. Kisan kiyashin da aka boye a cikin shekarun da suka gabata an nuna shi a fili.

Wannan ita ce dabarar da mai tunanin juyin juya hali daga Martinique, Frantz Fanon ya bayar. A cikin fitaccen littafinsa da ya yi na juyin juya hali, The Wretched of the Earth, Fanon ya rubuta cewa "kawar da mulkin mallaka ko da yaushe wani tashin hankali ne."

Shi ma shahararren malamin nan Falasɗinu Edward Said ya ce bai amince da hakan ba, inda ya ce amma Hamas ba ta wakiltar ƙungiyar mayaƙa masu neman 'yanci na zamani.

Batun jajircewa a kodayause yana zuwa ne da batun sojoji inda suke amfani da damar da suke da ita domin samun mulki. Hamas za ta samu damar watsi da mulkin mallaka idan ta yi nasara, kamar yadda Fanon ya bayyana. Isra'raila ta gano cewa Hamas babbar barazana ce a gareta shi yasa take son gamawa da ita baki ɗaya.

About the author: Ebrahim Moosa is the Mirza Family Professor of Islamic Thought & Muslim Societies in the Keough School of Global Affairs, at the University of Notre Dame in Indiana in the United States.

Disclaimer: The views expressed by the author do not necessarily reflect the opinions, viewpoints and editorial policies of TRT Afrika.

Game da marubucin: Ebrahim Moosa Farfesa ne kan Harkokin Musulunci da Al'ummomin Musulmi a Makarantar Sashen Harkokin Duniya, a Jami'ar Notre Dame da ke Indiana a Amurka.

Togaciya: Ba dole ba ne ra'ayin marubucin ya yi daidai da ra'ayi ko ka'idojin aikin jarida na TRT Afrika ba.

TRT Afrika