| Hausa
WASANNI
2 MINTI KARATU
Dan wasan Nijeriya Osimhen ya koma bakin aiki bayan ya kammala jinya
Koci Garcia ya ce za a ajiye Osimhen har sai lokacin babban wasan da za su fafata da Real Madrid ranar 29 ga watan Nuwamba.
Dan wasan Nijeriya Osimhen ya koma bakin aiki bayan ya kammala jinya
Osimhen ya ji rauni ne a wasan sada zumunta da Nijeriya ta yi da Saudiyya ranar 13 ga watan Oktoba, wanda aka tashi da ci 2-2./Hoto:AFP / Others
8 Nuwamba 2023

Kocin Napoli FC Rudi Garcia ya bayar da sanarwar dawowar dan wasan Nijeriya Victor Osimhen bakin fama, bayan ya yi jinyar kusan wata guda sakamakon raunin a ya ji a cinya.

Osimhen zai koma atisaye a yau Laraba amma ba zai fafata a wasan da tawagarsu za ta yi da Union Berlin na Gasar Zakarun Turai a Rukunin C, kamar yadda Garcia ya shaida wa taron manema labarai ranar Talata.

Osimhen ya ji rauni ne a wasan sada zumunta da Nijeriya ta yi da Saudiyya ranar 13 ga watan Oktoba, wanda aka tashi da ci 2-2.

Garcia ya ce Osimhen zai zauna a benchi har sai lokacin karawar da za Napoli za ta yi da Real Madrid ranar 29 ga watan Nuwamba a Rukunin C.

A halin yanzu Napoli tana mataki na biyu a Rukunin C a Gasar Zakarun Turai, inda take bayan Real Madrid da maki uku, don haka babu shakka fafatawar za ta yi zafi.

MAJIYA:TRT Afrika