Fidan ya ce mummunan shirin Isra'ila na rushe-rushe na tafiya afkawa Yammacin Gabar Kogin Jordan da Gabashin Kudus daga Gaza. /Hoto: AA

Ministan Harkokin Wajen Turkiyya Hakan Fidan ya jaddada buƙatar ƙara ƙaimi wajen jan hankalin ƙasashen duniya da su amince da Falasɗinu a matsayin 'yantacciyar ƙasa.

A ranar Lahadin nan Fidan ya ƙara da cewa jinkirta amincewa da Falasɗinu ba ya warware matsalar, sai dai ma ya bai wa Isra'ila ƙarin lokaci da dama.

Majiyoyin diflomasiyya sun bayyana cewa, Fidan ya aike da sakon a wajen Taron Kawayen Ƙasa da Ƙasa kan tabbatar da warware rikicin ta hanyar ƙasashe biyu, ciki har da amincewa da ƙasar Isra'ila da aka gudanar a Brussel.

A yayin taron farko, ƙasashe da hukumomin da ke bayar da taimako ga Falasɗinu sun fara ganawa da juna.

Firaministan Falasɗinu Mohammed Mustafa ya bayyana manufofin da gwamnatinsu ta sanya a gaba, yana mai bayyana abin da suke tsammanin gani daga ƙawayensu na duniya.

Taro na biyu ya tattauna kan batun ƙoƙarin da ake yi na warware rikicin Isra'ila da Falasɗinu a siyasance, da kuma ganin an kafa ƙasashe biyu masu 'yanci.

Shirin Isra'ila na kawar da Falasɗinawa daga bayan ƙasa

Fidan ya yi nuni da cewa daskarar da kuɗaɗen Falasɗinu da Isra'ila ta yi wata hanya ce ta tunzura mahukuntan Falasɗinu, ina ya nuna buƙatar kuɗaɗen gudanarwa da gwamnatin.

Ya jaddada ƙudirin Isra'ila ƙarƙashin gwamnatin Firaminista Benjamin Netanyahu mai tsaurin ra'ayi na kawar da Falasɗinawa gaba ɗaya daga doron ƙasa ta kowacce hanya.

Fidan ya kuma ce wannan mummunan shirin Isra'ila na rushe-rushe na tafiya afkawa Yammacin Gaɓar Kogin Jordan da Gabashin Ƙudus daga Gaza

Ya tunatar da dukkan ƙoƙarin da ake yi bayan ƙulla Yarjejeniyar Oslo, amma ya jaddada cewa ba tare da aiki da hanyoyi daban-daban ba, ba za a samu wani sabon sakamako mai kyau ba.

Falasɗinu ba a matsayin 'gwamnati' ba, sai matsayin 'hukuma' tun bayan Yarjejeniyar Oslo

Fidan ya yi tsokaci da cewa ƙasashen duniya sun zaɓi kiran Falasɗinu a matsayin 'hukuma' maimakon a kira ta da 'gwamnati' tun bayan Yarjejeniyar Oslo, inda yake nuna rashin adalci da yake ƙara ingiza mamayar da Isra'ila ke yi.

Ya jaddada buƙatar da ke akwai ta ganin Falasɗinu ta yi aiki a matsayin 'yantacciyar ƙasa mai cikakken iko, da ke da hukumominta da za su shawo kan waɗannan ƙalubale.

Ministan Harkokin Wajen na Turkiyya ya kuma nuna buƙatar samun ƙarin ƙasashe da za su amince da Falasɗinu, kuma su ce kar a sa ran lallai sai an Isra'ila ta tattauna da Falasɗinawa don zama 'yantacciyar ƙasa.

TRT World