Turkiyya ta jajanta wa Nijeriya game da fashewar wata motar dakon mai da ta yi sanadin mutuwar mutane da dama.
"Mun yi matukar bakin ciki da asarar rayuka da aka samu sakamakon fashewar tankar mai da ta afku a jiya a karamar hukumar Gurara ta Nijeriya," in ji ma'aikatar harkokin wajen Turkiyya a cikin wata sanarwa a ranar Lahadi.
Ma'aikatar ta miƙa ta'aziyyarta ga iyalan wadanda suka rasa rayukansu, tare da fatan samun sauki cikin gaggawa ga wadanda suka jikkata.
Adadin wadanda suka mutu sakamakon fashewar tankar mai a ranar Asabar da ta gabata a mahadar Dikko a jihar Neja ya kai 86, yayin da 55 suka samu raunuka, kamar yadda jami'ai suka tabbatar.
Jana'izar mutane da yawa
Abdullahi Baba-Arah, director-general of the Niger State Emergency Management
Abdullahi Baba-Arah, darakta-janar na hukumar ba da agajin gaggawa ta jihar Neja, shi ne ya ba da bayanan sabbin alkaluman, ya kuma kara da cewa an binne akasarin wadanda harin ya rutsa da su a wani kabari.
“An tabbatar da mutuwar mutane 86, tare da gano gawarwakinsu kuma an binne su. An binne mutum 80 a kabarin bai-daya a harabar cibiyar kula da lafiya a matakin farko ta Dikko, biyar kuma iyalansu ne suka binne su.
Bala'in ya afku ne a lokacin da wata motar dakon mai da ke matsanancin gudu ta ƙwace wa direban ta kuma yi hadari.
A lokacin da mazauna garin suka yi kokarin kwasar ganimar man da ke kwarara daga tankar da ta kife, sai wuta ta tashi a wajen, lamarin da ya rutsa da su, ciki har da masu aikin ceto.