'Yan sanda a Turkiyya sun kama mutum 44 waɗanda ake zargin 'yan ƙungiyar Daesh ne, kamar yadda majiyoyin tsaro suka tabbatar.
An gudanar da samame daban-daban a ranar Talata a kudu maso gabashin birnin Sanliurfa da tsakiyar lardin Konya domin kama waɗanda ake zargin.
Samame na baya-bayan nan da aka kai na daga cikin babban shirin Turkiyya na yaƙi da ta'addanci wanda samame ne da aka kai fiye da dubu ɗaya kan Daesh tun daga 1 ga watan Yunin 2023, inda aka kama sama da mutum 2,000 da ake zargi.
Waɗannan samamen na zuwa ne bayan wani hari da Daesh ɗin ta kai kan wata cocin Italiya, wanda hakan ya ja Turkiyyar ta ƙara matsa ƙaimi domin yaƙi da ta'addanci.
Turkiyya wadda tana daga cikin ƙasashen da suka soma ayyana Daesh a matsayin ƙungiyoyin ta'addanci tun daga 2013, na ci gaba da fuskantar barazana daga ƙungiyar, inda ta kai hare-hare da dama waɗanda suka yi sanadin mutuwar sama da mutum 300 da kuma jikkata da dama.
Haka kuma ƙungiyar ta ƙaddamar da hare-haren ƙunar baƙin-wake aƙalla goma da tayar da bam sau bakwai da kai hare-hare na makami huɗu a ƙasar.
Irin samamen da ƙasar ke kaiwa na nuni da irin sadaukarwar da Turkiyyar ta yi na tabbatar da zaman lafiya, hadin kai, da tsaron 'yan kasarta da kuma al'ummar duniya baki daya.