Masu binciken kufai (Archaelogist) a birnin Aizanoi na lardin Kutahya da ke kasar Turkiyya sun gano wasu kayan kwalliya ciki har da abin wuya da kayan kwalliya na mata na Daular Roma wadanda aka yi amfani da su fiye da shekara 2,000 da suka wuce.

An fi sanin birnin Aizanol da wurin tarihi na wurin ibada na Zeus a Anatolia kuma yana cikin jerin wuraren tarihi da Hukumar kiyaye Ilimi da Al'adu ta Majalisar Dinkin Duniya (UNESCO) ta ayyana a shekarar 2012.
Wani masani kan nazarin binciken kufai Gokhan Coskun, wanda ke Jami'ar Dumlupinar kuma jagoran binciken, ya ce a ranar Asabar an yi galibin aikin ne a kasuwar Agora wacce take gabas daga wurin ibada na Zeus.
Coskun ya ce tawagarsa ta gano shaguna masu shekara 2,000 a wata kasuwa. "Aikinmu bai takaita a cikin shagunan ba kawai. Ya kai ga hatta a kewayensu," in ji shi.

Yayin da yake bayyana irin kayan da aka gano, Coskun ya ce: "Daya daga cikin abubuwan da muka gano su ne kayan kwalliya masu kama da buroshi da hodar kwalliyar da ake sa wa a kasan gira wato abin da ake kira Eyeshadow a yau.
Coskun ya bayyana farin cikinsa kan binciken.
"Mun tabbatar da cewa wajen da muka gano shago ne da ke sayar da kayan kwalliya kamar turare da abin wuya da sauransu. Yayin tono kayan, mun gano kwalaben turarurruka da dama. Bayan su mun gano abin wuya. Ciki har da jigida da tsarkokin mata," in ji shi.

Coskun ya tabbatar da cewa kayayyakin ragowar kayan kwalliyar matan daular Roma ne.