Fadar shugaban kasar Turkiyya ta ce shugabannin biyu za su gudanar da taron manema labarai na hadin gwiwa bayan tattaunawarsu a Istanbul. / Hoto: Reuters

Shugaban kasar Ukraine Volodymyr Zelenskyy zai ziyarci kasar Turkiyya domin ganawa da shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan a ranar Juma'a.

Ganawar tasu za ta mayar da hankali ne kan kawo karshen yarjejeniyar jigilar hatsi daga Ukraine zuwa tekun Bahar Rum da kuma taron kungiyar tsaro ta NATO da za a yi a mako mai zuwa.

Shugabannin biyu dai suna son tsawaita yarjejeniyar da Majalisar Dinkin Duniya da Turkiyya suka kulla da Rasha wadda a karkashinta aka bai wa Ukraine damar jigilar hatsi zuwa kasuwannin duniya a lokacin yakin.

A ranar Alhamis ne Zelenskyy ya kama hanyarsa ta zuwa Prague domin ganawa da takwaransa na Czech Petr Pavel da sauran jami'ai, a daidai lokacin da ake ci gaba da yaki tsakanin Rasha da Ukraine, in ji kakakin shugaban Pavel.

Da farko dai, ya kai ziyara yankin Sofia don ganawa da jami'an kasar Bulgaria.

TRT World