Isra'ila na ci gaba da kashe Falasɗinawa a kullum a Gaza waɗanda akasarinsu yara ne da mata. / Hoto: AA

1611 GMT — Kafar watsa labaran Masar ta ce akwai alamun nasara a tattaunawar Gaza da Isra'ila

Kafofin watsa labaran Masar sun kwarmata cewa akwai “ci gaba mai yawa” a kan batun tsagaita wuta tsakanin Isra’ila da Gaza.

Kafar watsa labarai ta Cairo 24 ta ce akwai batutuwa da dama da ɓangarorin suka cimma matsaya a kansu.

Ana sa ran nan ba da jimawa ba za a sanar da matsaya kan batun yarjejeniyar tsagaita wutar da ake sa ran ɓangarorin za su cimmawa

1013 GMT — Sojojin Isra'ila sun afka birnin Deir Al-Ghusun na Falasɗinu

Sojojin Isra’ila a ranar Juma’a da dare sun afka birnin Deir Al-Ghusun wanda ke arewa maso gabashin birnin Tulkarm a Gaɓar Yamma da Kogin Jordan da Isra’ila ta mamaye, kamar yadda kafofin watsa labaran Isra’ila suka ruwaito.

Kamfanin dillancin labarai na Falasɗinu WAFA ya ruwaito cewa “Dakarun Isra’ila na musamman sun yi wa wani gida a Deir al-ghusun ƙawanya a daidai lokacin da ake ci gaba da musayar wuta.”

Aƙalla Falasɗinawa 491 Isra’ila ta kashe da kuma raunata sama da 4,950 a Gaɓar Yamma da Kogin Jordan ɗin tun bayan soma kai hare-hare a Gaza a ranar 7 ga watan Oktoba.

0927 GMT — Tawagar Hamas na hanyar Masar domin tattaunawar sulhu

Ƙungiyar Hamas ta sanar da cewa tawagarta na kan hanyar zuwa birnin Alkahira na Masar domin tattaunawa kan yarjejeniyar tsagaita wuta, a daidai lokacin da Majalisar Ɗinkin Duniya ke gargaɗin cewa barazanar da Isra'ila ke yi na afka wa Rafah kan iya jawo "zubar jini".

Masu shiga tsakani na ƙasashen waje na ta jiran ƙungiyoyin Falasɗinu su mayar da martani dangane da buƙatar tsagaita wuta tsawon kwanaki 40 domin musayar fursunoni.

Sakataren Harkokin Wajen Amurka Anthony Blinken shi ma ya ƙara jaddada matsayar Amurka kan rashin amincewa da batun afka wa Rafah, inda ya ce Isra'ila ba ta gabatar da wani tsari na kare farar hula ba da ke neman mafaka a can ba.

AA
AFP
AP
Reuters