Falasdinawa suna tono gawarwakin iyalan al Meghari da aka kashe a harin da Isra'ila ta kai sansanin 'yan gudun hijira na Bureij a Gaza/ Hoto: AP

1529 GMT Mutuwar fararen hula a Gaza 'abu ne mara misaltuwa da ba a taba yin irinsa ba — Guterres

Shugaban Majalisar Dinkin Duniya ya yi Allah wadai da abubuwan da suka faru a Gaza tun ranar 7 ga watan Oktoba a Gaza, yana mai cewa ana yi wa kisan gillar da ba a taba ganin irinsa ba tun bayan da ya hau mulki.

"Muna ganin kashe fararen hula marar misaltuwa da ba a taba yin irinsa ba a duk wani rikici tun lokacin da na Sakatare Janar,” Guterres ya fada a birnin New York yayin gabatar da sabon rahoton muhalli na Majalisar Dinkin Duniya.

Yana da matukar muhimmanci a iya sauya wannan bala'in zuwa wata dama, in ji Guterres, yana mai karawa da cewa: "Yana da matukar muhimmanci bayan yakin, mu matsa cikin azama, da kuma hanyar da za a bi wajen warware rikicin ta hanyar samar da kasashe biyu masu cin gashin kansu.

1221 GMT — Mutane da dama sun mutu a harin bama-bamai da Isra'ila ta kai wata makaranta — Hamas

Sama da mutum 10 ne suka mutu a wani harin da Isra’ila ta kai kan wata makaranta da Majalisar Dinkin Duniya ke kula da ita a sansanin ‘yan gudun hijira na Bureij a Gaza, in ji kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas.

A cikin wata sanarwa da Hamas ta fitar ta ce "Wannan mummunan laifi ne kuma rashin kunya ga hukumar kula da Falasdinawa 'yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya UNRWA da kuma Majalisar Dinkin Duniyar."

Ta yi kira da a dauki matakin gaggawa don "dakatar da hare-haren da ake kai wa fararen hula a makarantun da aka kare karkashin dokokin kasa da kasa."

Kawo yanzu dai babu wani bayani daga rundunar sojin Isra'ila kan wannan sanarwa.

1345 GMT — China za ta karbi bakuncin ministocin wajen kasashen Larabawa don tattauna batun tsagaita wuta a Gaza

Babban jami'in diflomasiyyar kasar China ya yi maraba da ministocin harkokin wajen kasashen Larabawa hudu da na Indonesiya a birnin Beijing, yana mai cewa kasarsa za ta yi aiki tare da "'yan'uwanmu maza da mata" na kasashen Larabawa da na Musulunci wajen kokarin kawo karshen yakin Gaza da wuri-wuri.

Ministocin kasashen waje daga Saudiyya da Masar da Jordan da Hukumar Falasdinu da Indonesiya sun zabi fara rangadi da wakilan dindindin a kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya a birnin Beijing a ranar Litinin din da ta gabata, lamarin da ke nuni da yadda China ke ƙara yin tasiri a fannin siyasa da kuma goyon bayan da ta daɗe tana bai wa Falasdinawa.

Wannan rangadin na da nufin sa ƙaimi ga tsagaita wuta da kuma ciyar da harkokin siyasa gaba da nufin samar da zaman lafiya mai dorewa, da kuma daukar nauyin mamayar Isra'ila kan keta haddi da laifuffukan da ake yi a Gaza da kuma mamayar yammacin Gabar Kogin Jordan, a cewar wata sanarwa da Ma'aikatar Harkokin Wajen Saudiyya ta fitar a shafinn X.

1305 GMT — Isra'ila ta kashe Falasdinawa 17 a kusa da wani asibiti

Akalla Falasdinawa 17 Isra’ila ta kara kashewa a harin da ta kai ta sama a kusa da Asibitin Yousef El Najar da ke kudancin Gaza, kamar yadda wadanda suka shaida lamarin suka tabbatar.

Jiragen yaki sun kai hari kan gidaje biyu da ke kusa da asibitin a birnin Rafah, kamar yadda shaidu suka tabbatar.

“Jiragen yakin Isra’ila sun kai hari kan gidajen da asuba, inda suka yi babbar barna a yankin,” kamar yadda wani da ya shaida lamarin ya bayyana wa kamfanin dillancin labarai na Anadolu.

0925 GMT — Hamas ta musanta rahoton musayar fursunoni tsakaninta da Isra'ila

Wani babban jagoran Hamas ya musanta rahotannin da ke cewa kungiyar ta Hamas ta cimma yarjejeniyar musayar fursunoni da Isra’ila.

“Rahotanni kan batun musayar fursunoni ba gaskiya bane,” in ji Izzat al Rishq a wata sanarwa da ta fitar.

Duka bangarorin na rike da fursunonin yaki wadanda suka kama. / Hoto: Reuters

Haka kuma wasu jaridun Isra’ila sun musanta wannan zargin na musayar fursunoni. “Babu komai har yanzu,” kamar yadda jaridar Post ta Birnin Kudus ta ruwaito jami’in na Isra’ila yana cewa.

0425 GMT — Isra'ila ta yi luguden wuta a Asitibin Indonesia da ke arewacin Gaza, ta kashe mutane da dama

Falasdinawa akalla takwas ne suka mutu yayin da gomman suka jikkata sakamakon luguden wuta da aka Isra'ila ta yi da makamai masu linzami a Asibitin Indonesia da yankunan da ke kusa da shi a areacin Gaza, a cewar wasu majiyoyi na asibitin,, baya ga bude wuta da Isra'ila ta yi kan duk mutumin da ya yi yunkurin fita daga asibitin.

Majiyoyin sun kara da cewa dakarun Isra'ila sun yi ta barin wuta a hawa na biyu na asibitin, lamarin da ya sa wurin ya lalace baki daya, sannan ta jikkata likitoci biyu a yayin da suke aiki.

Sun kara da cewa adadin mutanen da Isra'ila ta kashe yayin harin yana karuwa, musamman bayan da ta katse wutar lantarki don haka yana da matukar wahala a iya yi wa mutane tiyata don ceto rayukansu.

Ganau sun ce hare-haren na Isra'ila sun sa wutar lantarkin asibitin ta katse bayan janaretocinta sun daina aiki.

 kara da cewa adadin mutanen da Isra'ila ta kashe yayin harin yana karuwa./Hoto: AA

1222 GMT — An kwashe bakwaini daga Asibitin Al Shifa yayin da Isra'ila ke ci gaba da kai wa Gaza hari

Akalla jarirai bakwaini 31 aka kwashe daga babban asibitin Gaza, kuma za a kai su Masar, in ji jami’an kiwon lafiya na Falasdinu, yayin da wasu da dama da suka samu munanan raunuka ke nan a makale a wurin kwanaki bayan da sojojin Isra’ila suka mamaye harabar.

Kakakin ma'aikatar lafiyar Medhat Abbas ya tabbatar da kwashe jarirai 30. Hukumar agajin agaji ta Red Crescent ta Falasdinu ta ce ta kwashe jarirai 31 tare da hadin gwiwar hukumomin Majalisar Dinkin Duniya.

Ta ce za a kai su asibitin da Hadaddiyar Daular Larabawa ke kula da shi a birnin Rafah da ke kan iyakar Masar.

Za a kai su asibitin da Hadaddiyar Daular Larabawa ke kula da shi a birnin Rafah da ke kan iyakar Masar. / Photo: Reuters

1902 GMT — Ministan Isra'ila ya nemi kasashen duniya 'su samar wa Falasdinawa matsugunai a wasu wuraren'

Wani ministan Isra'ila ya ce bai kamata kasashen duniya su bayar da kudade don sake gina yankin Gaza da Isra'ila ta lalata ba, maimakon haka gara su samar "da matsugunai bisa radin kai" ga Falasdinawa a fadin duniya.

Ministan leken asirin Isra'ila Gila Gamliel ya ce "zabi" daya bayan an gama yaƙin shi ne "samar da shirin sake tsugunar da Falasdinawa ta hanyar gina musu matsugunai bisa taimakon sa kai, saboda dalilai na jinƙai, a wajen Zirin Gaza.

A rubutun da ya yi a jaridar The Jerusalem Post, ya ce "maimakon a ba da kudi don sake gina Gaza ko kuma ga kungiyar UNRWA da ta gaza, kasashen duniya za su iya taimakawa wajen dakar nauyin sake tsugunar da jama'ar Gaza, tare da taimakawa al'ummar Gaza gina sabbin matsugunai a sabbin kasashen da suka karbi bakuncinsu."

"Hakan zai iya zama mafita ta nasara: nasara ga fararen hula na Gaza da ke neman rayuwa mafi kyau da nasara ga Isra'ila bayan wannan mummunan bala'i."

Hukumomin Falasdinu a Gaza da yankin Yammacin Kogin Jordan da aka mamaye, sun sha yin watsi da irin wadannan shawarwarin da jami'an Isra'ila ke bayarwa, suna masu cewa hakan kabilanci ne da kuma son kawar da al'ummar Falasdinawa.

1920 GMT — An sake kaseh 'yan jarida uku a hare-haren Is'ila a Gaza

An kashe shugaban wata fitacciyar cibiyar yada labarai a Gaza da wasu 'yan jarida biyu a karshen makon nan a hare-haren da Isra'ila ta kai a yankin, in ji 'yan uwansu, lamarin da ya ƙara yawan 'yan jarida da suka mutu a rikicin na makonni shida.

Kwamitin Kare 'Yan Jaridu (CPJ) mai hedkwata a birnin New York ya ce idan aka hada adadin wadanda suka mutu a karshen makon a yanzu yawan ƴan jaridan da suka mutu ya kai 48, tun daga ranar 7 ga watan Oktoba.

Kungiyar ta CPJ, wadda jerin sunayen da ta fitar ya kunshi ‘yan jaridun da aka kashe a bangarorin biyu na rikicin, duk da yake dai akasarin su a Gaza ne, ta ce takan nemi akalla majiyoyi biyu don tabbatar da kowace mutuwa.

Ta ce jerin sunayen wadanda aka kashe sun hada da Falasdinawa 43 da Isra’ilawa hudu da kuma dan Lebanon daya.

TRT Afrika da abokan hulda