Dakarun Isra'ila sun kashe akalla mutum uku sannan suka raunata 13 a hare-haren da suka kai da daddare a birnin Jenin da ke Gabar Yammacin Kogin Jordan da aka mamaye, a cewar Ma'aikatar Lafiya ta Falasdinawa.
Da safiyar nan ta Litinin rundunar sojin kasa ta Isra'ila ta ce tana kai "hare-hare a wuraren da 'yan ta'adda suke" a Jenin, sannan mazauna yankin sun ce an harba musu wani makami mai linzami ta sama wanda ya rusa wani gida.
Rundunar sojin ta ce tana gudanar "gagarumin farmaki na yunkurin kawar da ta'addanci" a wani yanki na birnin da kuma babban sansanin 'yan gudun hijira ko da yake ba ta yi karin bayani ba.
An kwashe watanni ana zaman dar-dar a Yammacin Kogin Jordan yayin da dakarun Isra'ila ke ci gaba da kai samame a garuruwan Falasdinawa.
Dakarun Isra'ila sun kashe Falasdinawa akalla 180 tun daga farkon wannan shekarar, a cewar Ma'aikatar Lafiya.
An kashe akalla 'yan Isra'ila 25 a hare-hare da daban-daban tun daga farkon bana.